Yadda Dakarun Sojoji Suka Hallaka 'Yan Ta'adda 2,245 da Ceto Mutum 1,993

Yadda Dakarun Sojoji Suka Hallaka 'Yan Ta'adda 2,245 da Ceto Mutum 1,993

  • Hedkwatar tsaro ta ƙasa (DHQ) ta bayyana nasarorin da dakarun sojojin Najeriya suka samu a yaƙin da suke yi da ƴan ta'adda a ƙasar nan
  • DHQ ta bayyana cewa daga watan Afirilu zuwa watan Yunin shekarar 2024, dakarun sojoji sun hallaka ƴan ta'adda 2,245
  • Sojojin sun kuma ceto mutum 1,993 daga hannun ƴan ta'adda tare da cafke mutum 3,682 da zargi da aikata ayyukan ta'addanci

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Hedikwatar tsaro ta ƙasa (DHQ) ta bayyana cewa, dakarun sojoji da ke aikin samar da tsaro a faɗin ƙasar nan sun kuɓutar da mutum 1,993 da aka yi garkuwa da su.

Dakarun sojojin sun kuma kashe ƴan ta'adda 2,245 tare da cafke mutum 3,682 da ake zargin ƴan ta'adda ne cikin watanni uku.

Kara karanta wannan

El Rufai, Ministan Tinubu da wasu ƴan Najeriya da suka mallaki gidajen alfarman N1.49trn a Dubai

Sojoji sun hallaka 'yan ta'adda 2,245
Sojoji sun ceto mutum 1,993 daga hannun 'yan ta'adda Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Twitter

Jaridar Leadership ta ce daraktan yaɗa labarai na DHQ, Manjo Janar Edward Buba ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis, wajen yiwa manema labarai ƙarin haske game da ayyukan sojojin daga watan Afirilu zuwa watan Yunin shekarar 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wace nasara sojoji suka samu kan ƴan ta'adda?

Manjo Janar Edward Buba ya ce a tsakanin watan Afrilu zuwa Yuni, sojojin sun kuma ƙwato makamai 2,783, alburusai 64,547 da ɗanyen mai na sata wanda kuɗinsa da ya kai N10,533,131,470.00, rahoton Daily Nigerian ya tabbatar.

Ya bayyana cewa makaman sun haɗa da bindigogi ƙirar AK47 guda 1,169, harsasai guda 36,273 na musamman masu kaurin 7.62mm, harsasai guda 14,764 na musamman ƙirar NATO masu kaurin 7.62mm, makamai guda 713 da alburusai guda 9,850.

Sauran sun haɗa da lita 9,225,149 na ɗanyen mai da aka sace, lita 2,874,916 na gas, lita 29,900 na dizal da lita 31,380 na man fetur da dai sauransu.

Kara karanta wannan

Kwankwaso zai fara gwabzawa da EFCC a kotu ana tsaka da rikicin sarautar Kano

Sojoji sun kuɓutar da mutane

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya a jihar Borno sun ceto mata bakwai da yara tara da ƴan ta'adda suka sace daga gidajensu.

An kuɓutar da mutanen ne a wasu jerin ayyukan yaƙi da ta’addanci da sojoji tare da haɗin gwiwar ƴan banga suka gudanar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel