'Yan Bindiga Sun Kai Mummunan Hari Ofishin Ƴan Sandan Ebonyi, an Kashe Mutane 5

'Yan Bindiga Sun Kai Mummunan Hari Ofishin Ƴan Sandan Ebonyi, an Kashe Mutane 5

  • Rahotanni sun bayyana cewa 'yan bindiga sun kai hari ofishin 'yan sandan Ishieke da ke jihar Ebonyi
  • An ce 'yan bindigar sun kai hari da daren ranar Laraba kuma an kashe mutum biyar a musayar wutar mintuna 30
  • Haka zalika, an ga wasu motoci guda biyu da aka babbake su, yayin da aka jefa al'ummar yankin cikin tashin hankali

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Ebonyi - Akalla mutane shida a wani hari da 'yan bindiga suka kai ofishin 'yan sanda na Ishieke da ke karamar hukumar Ebonyi, jihar Ebonyi.

An ruwaito cewa 'yan bindigar sun farmaki 'yan sandan misalin karfe 9:00 na daren ranar Laraba, inda suka bude wuta kan mai uwa da wani.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi yunƙurin takaita babban limamin Musulmi a jihar Kaduna

'Yan bindiga sun farmaki 'yan sanda a Ebonyi
An kashe mutane biyar a harin da ƴan bindiga suka kai ofishin ƴan sandan Ebonyi. Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

'Yan bindiga sun farmaki 'yan sanda

Wani ganau ya shaidawa Channels TV cewa jami'an yan sandan da ke ofishin a lokacin harin sun yi musayar wuta da ƴan bindigar na mintuna 30.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Amma an ce jami'an tsaro sun kai wa 'yan sandan dauki, a lamarin da ya jefa al'ummar yankin cikin tashin hankali da gudun ceton rai.

Wani faifan bidiyo da ya yadu a soshiyal midiya a safiyar ranar Alhamis ya nuna mutane biyar da aka kashe da ake zargin maharan ne.

Babu bayani daga rundunar 'yan sanda

Haka zalika, an ga wasu motoci guda biyu da aka babbake su, yayin da aka ce an garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa wani asibiti a Abakaliki, in ji rahoton Daily Post.

Sai dai har zuwa lokacin kammala wannan rahoton, rundunar 'yan sanda ba ta fitar da rahoto a hukumance kan farmakin ba.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai mummunan hari Masallaci, sun kashe bayin Allah a Zamfara

Amma an ce maharan sun kai farmakin ne awanni kadan bayan da uwar gidan Sufeta Janar, Elizabeth Egbetokun ta ziyarci Ebonyi domin ƙaddamar da shirin tallafi.

'Yan ta'adda sun kashe sojoji 21

A wani labarin, mun ruwaito cewa 'yan ta'adda da ake zargin 'yan kungiyar Al-Qaeeda ne sun kashe sojoji 21 da farar hula a ƙasar Nijar.

An ruwaito cewa 'yan bindigar sun kashe sojojin a wani harin kwanton ɓauna da suka yi masu a Tassia Sun Badjo, yankin Yammacin Tillaberi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel