Rikicin Manoma da Makiyaya Ya Jawo An Kashe Mutane da dama a Jigawa

Rikicin Manoma da Makiyaya Ya Jawo An Kashe Mutane da dama a Jigawa

  • Rundunar 'yan sandan jihar Jigawa ta tabbatar da kisan mutane uku a jihar Jigawa bayan ballewar rikicin manoma da makiyaya
  • Jami'in hulda da jama'a na rundunar, DSP Lawal Shiisu ya shaidawa Legit Hausa cewa an samu sabanin fahimta tsakanin makiyaya da manoma
  • Ya ce a baya gwamnati ce ta bayyana cewa an kwace wani kaso na gandun dajin daga hannun makiyaya tare da maido shi ga manoma

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Jigawa- Rikicin manoma da makiyaya a jihar Jigawa ya jawo asarar rayukan mutane uku a yankin gandun dajin Baranda da ke karamar hukumar Kiyawa.

Kara karanta wannan

Ruwa ya cinye wasu dalibai a hanyarsu ta dawo wa daga jarrabawa a Kaduna

Lamarin ya afku ne bayan an samu sabanin fahimta tsakanin makiyaya da manoma a yankin kan saboda furucin gwamnati.

Police
Mutane 3 sun rasu a rikicin makiyaya da manoma a Jigawa Hoto: Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Vanguard News ta wallafa cewa jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan jihar, DSP Lawal Shiisu ya tabbatar da lamarin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"An ceto wasu da raunuka," DSP Shiisu

Rundunar 'yan sandan Jigawa ta bayyana cewa an samu ceto wadansu da rikicin manoma da makiyaya ya rutsa da su a jihar.

Pulse Nigeria ta wallafa cewa sun ceto mutane uku da raunuka daban-daban, sannan an ceto wasu guda shida da ake dab da kai wa hari.

Jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan Jigawa, DSP Lawal Shiisu ya tabbatarwa Legit Hausa cewa ba a kama kowa ba kan lamarin.

Za a warware rashin fahimtar makiyaya-manoma?

Rundunar 'yan sandan Jigawa ta bayyana cewa yanzu haka ana gudanar da taron kusoshin gwamnati kan rashin fahimtar da ta jawo rikicin manoma a jihar.

Kara karanta wannan

An shiga rudani, 'yan ta'adda sun lafta harajin wata wata a kan mazauna Binuwai

DSP Lawal Shiisu Abdullahi ya shaidawa Legit Hausa cewa an samu rikicin ne saboda tunanin gwamnati ta kwace burtalai kuma an mayar da su ga manoma.

Ya ce yanzu haka za a bambance wa makiyayan da manoman wurin da aka kwace a gandun dajin, da wuraren da har yanzu burtalai ne.

An kashe mutane a rikicin Jigawa

A baya mun ruwaito cewa rikicin manoma da makiyaya ya yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla guda biyar a jihar Jigawa.

Jami'in hulda da jama'a na rundunar, DSP Lawal Shiisu ya ce lamarin ya afku a dajin Hayin Kogi da ke karamar hukumar Birnin Kudu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Online view pixel