Rikicin Sarauta: Kotu ta Haramtawa Gwamnatin Sokoto Tsige Hakimai

Rikicin Sarauta: Kotu ta Haramtawa Gwamnatin Sokoto Tsige Hakimai

  • Babbar kotun a Sokoto ta dakatar da yunkurin sauke hakimai guda uku a yayin da dambarwar masarautar jihar ta yi kamari a yanzu
  • Kotun ta yanke hukuncin ne bayan wasu hakimai guda biyu daga cikin 15 da gwamnatin ta dakatar su ka kai kara wajen alkali
  • Lamarin na zuwa ne a lokacin da ake rikici kan kokarin da kungiyar kare hakkin musulmi ta kasa ta koka kan cire Sarkin musulmi

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Sokoto- Yayin da rikicin masarauta ke kara kamari a Sokoto, babbar kotun jiha ta dakatar da gwamna Ahmed Aliyu daga tsige hakimai biyu da ta dakatar a baya.

Kara karanta wannan

Ruwa ya cinye wasu dalibai a hanyarsu ta dawo wa daga jarrabawa a Kaduna

Hakiman na daga cikin masu rike da sarautu 15 da gwamnatin Sokoto ta dakatar daga kujerunsu a baya bisa wasu dalilinsu.

Sokoto
Kotu ta dakatar da gwamnatin Sokoto kan sauke hakimai Hoto: Hoto: @Ahmedaliyuskt
Asali: Twitter

Punch News ta wallafa cewa hakiman Tambuwal, Buhari Tambuwal da na Kebbe, Abubakar Kassim ne su ka nemi kotu da dakatar da gwamnatin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Kowa ya tsaya a matsayarsa a Sokoto," Kotu

Mai shari'a Kabiru Ibrahim Ahmed ya umarci gwamnatin jihar Sokoto da ta dakata da duk wani yunkurin tsige sarakuna.

Haka kuma kotun ta umarci fadar sarkin musulmi ta dakata da duk wani yunkuri da ta ke kokarin yi kan masarautun, Solace Base ta wallafa.

An takawa gwamnatin Sokoto burki

Gwamnatin jihar Sokoto dai ta yi yunkurin tsige wasu masu rike da sarautun gargajiya bisa zargin rashin biyayya.

A baya majalisar dokokin jihar ta kori masu rike da sarautar gargajiya 15, kuma sun samar da dokar da za ake ganin zai tsige sarkin musulmi.

Kara karanta wannan

Kotu ta yanke hukunci kan Emefiele, an gano miliyoyin daloli da aka wawushe

Tuni lamarin ya yamutsa hazo har ta kai mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima, ya gargadi gwamnatin Sokoto kan yunkurin.

Shettima ya yi gargadin tsige Sultan

A wani labarin kun ji cewa mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya gargadi gwamnatin jihar Sokoto kan tsige sarkin musulmi.

Kungiyar kare hakkin musulmi (MURIC) ce ta yi ikirarin cewa akwai makarkashiyar tube rawanin Sarkin musulmin, Muhammad Sa'ad Abubakar III.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Online view pixel