Zaman Lafiya: Rundunar Sojoji Ta Bude Kofa Domin Yin Sulhu da ’Yan Bindiga

Zaman Lafiya: Rundunar Sojoji Ta Bude Kofa Domin Yin Sulhu da ’Yan Bindiga

  • Rundunar sojin Najeriya ta yi kira na musamman ga kungiyoyin 'yan ta'adda da tsagerun da suka dauki makami domin yaki da gwamanti
  • Babban hafsun sojojin Najeriya, Laftanal Janar Taoreed Lagbaja ne ya yi kiran a jiya Laraba yayin wata ziyarar aiki da ya kai a jihar Bauchi
  • Laftanal Janar Taoreed Lagbaja ya kuma yi kira na musamman ga jami'an soji kan yadda za su cigaba da yaki da ƴan bindiga a Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Bauchi - Babban hafsun dakarun Najeriya Laftanal Janar Taoreed Lagbaja ya yi kira na musamman ga 'yan bindiga.

Laftanal Janar Taoreed Lagbaja ya bayyana hanyoyin da yan bindigar ya kamata su bi maimakon daukar makami.

Kara karanta wannan

'Ana shan wuya,' Wani babba a APC ya cire kunya ya koka kan mulkin Tinubu

shugaban soji
Rundunar soji ta yi kira ga 'yan bindiga. Hoto: HQ Nigerian Army
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa hafsun ya yi kiran ne a jiya Laraba yayin da ya kai ziyarar aiki a jihar Bauchi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me ya kamata yan bindiga su yi?

Laftanal Janar Taoreed Lagbaja ya ce ya kamata yan bindiga su tuba sun nemi tattaunawa da hukumomin Najeriya maimakon daukar makami.

Hafsun sojojin ya kara da cewa dukkan wanda ya ji an yi masa ba daidai ba, kamata ya yi ya nemi hanyar warware matsalar ba ta yaki da kasa ba.

Ya kara da cewa matukar babu zaman lafiya to dukkan abin da suke nema a wajen gwamnati ba lallai su samu ba, rahoton This Day.

Janar Lagbaja ya karfafi sojojin Najeriya

Babban hafsun ya yi kira ga daukacin sojojin Najeriya kan cigaba da aiki domin bayar da tsaro a kasa baki daya.

Kara karanta wannan

An canza salo: Gwamnatin Najeriya ta fitar da bayanai kan yi wa yan bindiga tarko

Laftanal Janar Taoreed Lagbaja ya ce suna sane da dukkan matsalolin da dakarun rundunar ke fuskanta kuma suna ƙoƙarin daukan mataki.

Ya ce akwai matsalolin karin matsayi da samun albashi a kan lokaci wanda a yanzu haka ana ƙoƙarin magancesu.

An kama barawo a jihar Bauchi

A wani rahoton, kun ji cewa rundunar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Bauchi ta cafke babban ɓarawo da ake zargin ya fitini al'umma da sace-sace.

Mutumin da ake zargi mai suna Glory Samuel ya sace makudan kudi da kayayyaki na miliyoyin kudi daga mutane da dama a jihar Bauchi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng