Kaduna: Rundunar Sojojin Najeriya ta Samar da Hanyar Magance Rashin Tsaro

Kaduna: Rundunar Sojojin Najeriya ta Samar da Hanyar Magance Rashin Tsaro

  • Rundunar sojojin Najeriya ta samar da wasu hanyoyin rage hanyoyin magance rashin tsaro da ya addabi al'ummar jihar Kaduna
  • Rundunar ta samar da karin rundunonin sojoji da sansanin sojojin sama a yankunan Samaru Zango-Kataf, Giwa da Birnin-Gwari
  • Tuni kungiyar 'yan jaridu na kudancin Kaduna su ka yi maraba da matakin da su ke ganin zai kawo sauki ga halin da jama'a ke ciki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Kaduna- Matsalolin rashin tsaro a jihar Kaduna ya sanya rundunar sojojin kasar nan kara daukar mataki domin magance matsalar.

Rundunar ta kara samar da sansanin sojoji a yankuna daban-daban na jihar domin kara karfin jami'an tsaron wajen yakar ta'addanci.

Kara karanta wannan

Yayin da ake rade radin tuge shi, Sultan ya tura sako ga rundunar sojoji

Uba Sani
An kara sansanin sojoji a Kaduna saboda rashin tsaro Hoto: Senator Uba Sani
Asali: Facebook

Sojoji za su inganta tsaro a jihar Kaduna

Daily Trust ta wallafa cewa an samar da rundunoni guda uku a yankunan Samaru Zango-Kataf, Giwa da Birnin-Gwari.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rundunar sojojin saman kasar nan za ta samar da sansanin sojoji a Millennium City da ke karamar hukuma Chikun a Kaduna.

Wannan na zuwa ne kwanaki kadan bayan kammala taron jihohin Arewa maso yamma kan magance matsalar tsaro, Nigerian Tribune ta wallafa.

Mutanen jihar Kaduna sun yi murna

A martanin da su ka yi kan samar da sansanin sojoji a yankunan Kaduna, kungiyar 'yan jarida na Kaduna ta Kudu sun yaba da hadin kan gwamna Uba Sani da rundunar tsaro.

A sanarwar da shugaba da sakataren kungiyar, Ango Bally da Lilian Silas su ka sanyawa hannu, sun ce hakan zai taimaka wajen rage rashin tsaro.

Kara karanta wannan

An kama ɗan damfara da sunan samawa mutane aikin soja, rundunar soji ta yi karin haske

Sojoji sun yi galaba kan miyagu

A baya kun ji cewa sojoji sun samu nasarar dakile ayyukan 'yan ta'adda a wasu jihohin Arewacin Najeriya da su ka hada da Kaduna da Filato.

Jami'in hulda da jama'a na rundunar da ke atisayen OPSH, Manjo Samson Zhakom ya ce sojojin sun kwato bindigogi da dama da suka hada da AK47.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.