An Shawarci Gwamnati Ta Bude Iyakokin Shigo da Abinci Domin Magance Yunwa a Najeriya
- Hukumar kare hakkin masu sayayya a kasa sun bukaci gwamnatin tarayya ta bude iyakokin kasar nan domin shigo da abinci cikin Najeriya
- Mukaddashin shugaban hukumar, Adamu Abdullahi da ya bayyana haka a Bauchi ya ce idan aka bari a shigo da abinci ta halastacciyar hanya, zai rage yunwa
- Ya kuma ce su na sanya idanu kan hauhawar farashi a kasuwannin Najeriya, dan haka ne ya shawarci al'umma su sanar masu da duk wasu kaya na bogi
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Abuja- Hukumar kula da kiyaye hakkin masu sayayya (FCCPC) ta shawarci gwamnatin tarayya ta buɗe iyakokin kasar nan domin shigo da kayan abinci ta halastacciyar hanya.
Hukumar na ganin ta hanyar bari a shigo da kayan abinci ne kawai za a rage yunwar da ta addabi 'yan Najeriya.
Nigerian Tribune ta wallafa cewa mukaddashin shugaban hukumar, Adamu Abdullahi ne ya bayyana bukatar bude iyakokin kasar a Bauchi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hauhawar farashi da yunwa a Najeriya
Hukumar kare hakkin masu saye ta Najeriya ta ce ta na sanya idanu kan yadda ake samun hauhawar farashi a kasuwannin kasar nan.
Mukaddashin shugaban hukumar, Adamu Abdullahi ne ya bayyana haka a wani taro da ya gudana a dakin taron fadar Bauchi, jaridar Independent ta wallafa.
Ya ce su na ganin yadda farashin kaya ke hawa a kasuwanni, kuma za su tabbata ba a rika shiga hakkin masu sayen kaya ba.
Ya ce yanzu haka su na wayar da kan jama'a kan tsawwala farashi kan kayayyakin da su ke sayarwa jama'a.
Mukaddashin shugaban ya ce sun je jihar Bauchi ne domin wayar da kai kan yadda za a gane kaya marasa inganci da hanyoyin da za a sanar da hukumomi domin daukar mataki.
Masarauta ta magantu kan hauhawar farashi
Sarkin Bauchi, Dr. Rilwanu Sulaiman Adamu ya bayyana rashin jin dadi kan yadda ake samun hauhawar farashin kayayyaki a kasuwanni.
Sarkin, wanda hakimin Lame, Yakubu Aliyu Lame ya wakilta ya ce akwai bukatar gwamnati ta gaggauta samar da hanyoyin sauko da farashin domin 'yan kasa na shan wahala
Tsohon minista ya nemi kara albashi
A wani labarin kun ji cewa tsohon ministan ayyuka a gwamnatin Muhammadu Buhari, Babatunde Raji Fashola ya shawarci gwamnatin Bola Tinubu ta gaggauta kara albashin ma'aikata.
Ya ce yan Najeriya na fama da rashin abin hannu da hauhawar farashin kayayyaki a kasuwanni, saboda haka ya ga dacewar kara albashin.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng