Ana Cikin Matsalar Rashin Tsaro, Shettima Ya Fadi Shirin Tinubu Kan 'Yan Bindiga

Ana Cikin Matsalar Rashin Tsaro, Shettima Ya Fadi Shirin Tinubu Kan 'Yan Bindiga

  • Kashim Shettima ya yi magana kan matsalar rashin tsaron da ta daɗe tana cin tuwo a ƙwaryar al'ummar Najeriya
  • Mataimakin shugaban ƙasan ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu ya ƙudiri aniyar magance matsalar rashin tsaron da ƙasar nan ke fama da ita
  • Ya buƙaci ƴan Najeriya da su marawa shugaban ƙasan baya domin ganin an samu nasarar kawo ƙarshen matsalar rashin tsaron

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Mataimakin shugaban ƙasa, Sanata Kashim Shettima, ya yi magana kan shirin Bola Tinubu na kawo ƙarshen matsalar rashin tsaro.

Kashim Shettima ya bayyana cewa shugaban ƙasan ya ƙudiri aniyar magance ɗumbin kalubalen tsaro da ƙasar nan ke fuskanta.

Shettima ya fadi kudirin Tinubu kan rashin tsaro
Shettima ya ce Tinubu na son kawo karshen rashin tsaro Hoto: @OfficialSKSM
Asali: Twitter

Kashim Shettima a jihar Kano

Kara karanta wannan

ASUU ta tsorata Gwamnatin Bola Tinubu, an fara zaman tattaunawa a Abuja

Kashim Shettima ya bayyana haka ne a Kano a lokacin da ya karɓi baƙuncin wata tawaga ta shugaban ƙasa domin ta’aziyyar rasuwar surukarsa, Hajiya Maryam Albishir.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun bakinsa, Stanley Nkwocha ya sanya a shafinsa na X a ranar Laraba.

Me Shettima ya ce kan shirin Tinubu?

Da yake yabawa ziyarar, mataimakin shugaban ƙasan ya sake nanata abin da ya bayyana a matsayin jagoranci na gaskiya na Tinubu, yana mai cewa shugaban ƙasan na nufin ƙasar nan da alheri.

"Komai nisan dare, gari zai waye. Tabbas muna fuskantar ƙalubalen tsaro a faɗin ƙasar nan, amma shugaban ƙasa a shirye yake wajen sauya ma'anar mulki na zamani, da jajircewa wajen magance matsalar rashin tsaron da ke addabar ƙasar nan."

Kara karanta wannan

NLC: Ƴan kwadago sun roki Tinubu, sun faɗi mafi ƙarancin albashin da suke buƙata

"Ina so na yi kira a garemu da mu mara masa baya kan wannan ƙudirin na sa domin mu ceto ƙasar nan a tare.
Ba batun ɗora alhaki kan wasu ba ne. Batu ne na tabbatar da cewa ƙasar nan ta yi aiki, sannan idan Najeriya ta yi aiki, Afirika za ta yi aiki."

- Kashim Shettima

Shettima ya nuna matuƙar godiyarsa ga gwamnati da al’ummar jihar Kano bisa karɓar baƙuncinsa da iyalansa na tsawon kwanaki uku.

Saƙon Shettima kan batun tsige Sarkin Musulmi

A wani labarin kuma, kun ji cewa mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya gargaɗi gwamnatin jihar Sokoto kan yunƙurin da ta ke yi na cire Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III daga muƙaminsa.

Mataimakin shugaban ƙasan ya bayyana cewa mai alfarma Sarkin Musulmin ba wai kawai Sarki ba ne a Sokoto, darajarsa da ƙimarsa sun wuce hakan.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel