Mutanen Zamfara Sun Barke da Murna Dogo Gide Ya Dawo Yankinsu, Sun Rera Masa Waka

Mutanen Zamfara Sun Barke da Murna Dogo Gide Ya Dawo Yankinsu, Sun Rera Masa Waka

  • Al'ummar yankin Magami da ke karamar hukumar Gusau sun barke da murna bayan Dogo Gide ya dawo yankinsu
  • Mazauna garin sun tabbatar da cewa Dogo Gide ya ba da umarnin dakatar da kama jama'a domin a yi noma a yankin
  • Wannan na zuwa ne bayan fitar da rahotanni cewa Dogo Gide ya mutu wanda babu tabbaci a hukumance

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Zamfara - Wasu mazauna wani yanki a jihar Zamfara sun barke da murna bayan rikakken dan ta'a'dda, Dogo Gide ya dawo yankinsu.

Al'ummar yankin Magami a karamar hukumar Gusau sun nuna jin dadinsu kan lamarin inda suke wakokin nuna farin ciki.

Kara karanta wannan

Rikici ya kaure tsakanin masu nadin sarauta, an shafe shekaru 4 babu Sarki

Mazauna wani yanki a Zamfara sun yi murna da dawowar Dogo Gide yankinsu
Mazauna Magami a jihar Zamfara sun ji dadin dawowar Dogo Gide yankinsu saboda samun damar noma. Hoto: HQ Nigerian Army.
Asali: Facebook

Zamfara: Ana murna Dogo Gide ya dawo

An ruwaito a baya cewa Dogo Gide ya rasa ransa amma sai dai a lokacin rundunar sojoji ba ta tabbatar da mutuwar ba a hukumance, cewar Premium Times.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Masu mazauna yankin sun tabbatar da cewa Dogo Gide ya dawo kauyen Kizara da ke kusa da Magami inda ya umarci al'umma su ci gaba da noma.

Gide ya ba da umarnin ne tare da tabbatar musu da cewa kada kowa yaji tsoron garkuwa ko kwace musu dukiyoyi.

An rera wakokin murnar ganin Dogo Gide

Hakan ya jawo rera wakoki na murna bayan dawowar Gide yankin saboda ci gaba da noma ba tare da katsalandan ba.

"Mazauna yankin suna murna ne saboda an dakatar da kisa da kama mutane da kuma neman kudin fansa."
"An bar gonaki na tsawon shekaru hudu babu noma amma yanzu an fara noma saboda umarnin da Dogo Gide ya bayar."

Kara karanta wannan

Rikicin manoma da makiyaya ya jawo an kashe mutane da dama a Jigawa

"Dogo Gide ya zauna da Fulani har da Ado Aliero inda ya gargade su da su dakatar da kama mutane su bar jama'a su yi noma."

- Cewar majiyar

Babu gaskiya kan mutuwar Dogo Gide

Kun ji cewa bayan sanar da mutuwar Dogo Gide a ranar Laraba 27 ga watan Maris da ake yadawa a kafofin sadarwa ya tabbata karyane.

An yaɗa cewa dan bindigan ya mutu ne yayin da yake karɓar kulawa a wani asibiti mai zaman kansa a jihar Sokoto.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel