Gobara Ta Kama a Matatar Man Dangote, Kamfanin Ya Yi Martani Kan Lamarin
- Wani bangare na matatar man Alhaji Aliko Dangote ya kama da wuta a jihar Lagos a yau Laraba 26 ga watan Yunin 2024
- Wutar ta tashi ne bangaren ETF da ke tace gurbataccen ruwan matatar inda aka tabbatar da kashe wutar da gaggawa
- Kakakin kamfanin, Anthony Chiejina shi ya tabbatar da haka inda ya ce babu rasa rai ko rauni da aka samu daga musifar
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Lagos - An shiga tashin hankali bayan wani bangare na matatar man Aliko Dangote ya kama da wuta.
Lamarin ya faru ne a yau Laraba 26 ga watan Yunin 2024 a sashen tsaftace ruwa na matatar da ake kira ETF.
Lagos: Matatar Dangote ta kama da wuta
Kakakin kamfanin Dangote, Anthony Chiejina shi ya tabbatar da haka a shafin X a yau Labara 26 ga watan Yunin 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Chiejina ya ce wutar ta kama ne a bangaren ETF da ke tace girbataccen ruwa a matatar da ke jihar Lagos.
Ya tabbatar da cewa an shawo kan matsalar inda ya ce ba wata babbar matsala ba ce kuma babu asara.
Martanin kamfanin Dangote kan iftila'in
"Mun yi nasarar shawo kan matsalar wutar da yake ba babba ba ce a yau Laraba 26 ga watan Yunin 2024 a sashen ETF."
"Ba wani abin damuwa ba ne tun da matatar na ci gaba da aiki kuma babu rauni ko mutuwa daga bangaren ma'aikatanmu."
- Anthony Chiejina
Wani mai amfani da shafin X, @Imranmuhdz a wallafa faifan bidiyon yadda gobarar ta kama ta ke ci inda mutane da dama suka yi martani.
Gwamnati ta kalubalanci Aliko Dangote
A wani labarin, kun ji cewa Gwamnatin tarayya ta ce babu wani gurbataccen mai da ake shigo da shi Najeriya, yayin da take martani ga wani jami'in matatar man Dangote.
Gwamnatin ta yi wannan maganar ne a ranar Talata a wajen taron ganawarta da dillalan man fetur a babban birnin tarayya Abuja
Taron ya mayar da hankali kan kudin man da aka tace, kalubale da kuma matsalar shigo da kayayyakin da ake sarrafa su a Najeriya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng