Matsalar Tsaro: Gwamnonin Arewa Sun Tsara Hanyar Murƙushe Ƴan Bindiga
- Gwamnonin Arewa maso Yamma sun ce sun samar da tsarin magance matsalar tsaro a shiyyar da lokacin da zai dauka
- Gwamnan jihar Katsina ya bayyana hakan a karshen taron kwana biyu kan tsaro da shirin UNDP ya shirya a Katsina
- Malam Dikko Umaru Radda ya ce nan na mako uku za a kaddamar da sakatariyar da za ta tabbatar da aiwatar da tsarin
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Jihar Katsina - Gwamnonin Arewa maso Yamma sun amince da wani tsari da wa'adi na kawo karshen matsalar tsaron da ta addabi shiyyar.
Shugaban ƙungiyar gwamnonin shiyyar, Gwamna Dikko Umaru Radda ya bayyana hakan a karshen taron tsaro da zaman lafiya na shiyyar da ya gudana a Katsina.
Mai tallafawa gwamnan Katsina ta fuskar kafofin sada zumunta, Isah Miqdad ya sanar da hakan a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An samo hanyar inganta tsaro a Arewa
Sanarwar ta ce gwamnonin Arewa maso Yamma sun cimma matsayar ne bayan tattaunawarsu da hukumomin Majalisar Dinkin Duniya.
Malam Dikko Radda ya ce nan da mako uku za a kaddamar da wata sakatariya wanda za ta samar da faffaɗan tsari da zai cimma yarjejeniyar tsaron.
A cewar Gwamna Radda, tsarin da aka amince da shi zai sa kowanne gwamna ya aiwatar da dabarun magance tsaro da aka amince da su a wajen taron.
Gwamnonin Arewa maso Yamma sun haɗa kai
Shugaban ƙungiyar gwamnonin ya ce taron kwana biyun da aka yi ya zakulo ainihin inda matsalar tsaro take a Arewa maso Yamma, da hanyar magance ta.
Gwamnan na Katsina ya ce an tattauna kan kalubalen da jihohin ke fuskanta wajen dakile rashin tsaro kuma an samar da mafita kan hakan.
Malam Radda ya ba da tabbacin cewa gwamnonin Arewa maso Yamma za su yi duk mai yiwuwa na ganin an kawo karshen tashe tashen hankula a shiyyar.
Gwamnan Katsina ya godewa majalisar UN
Sai dai ya ce ba za a iya cimma wadannan tsare tsare ba har sai an fara duba batun bunkasa tattalin arziki wanda shi ne ginshikin dakile matsalar tsaro.
Gwamnan ya godewa UN da shirin UNDP na shirya wannan taron tare da hadin guiwar gwamnonin Arewa maso Yamma da masu ruwa da tsakin da suka halarta.
Baya ga matsalar tsaro, an tattauna batutuwan da suka shafi samar da abinci, bunkasa tattalin arziki da kuma inganta rayuwar al'ummar shiyyar.
Tsaro: Gwamnonin Arewa sun je Amurka
A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnonin Arewa sun garzaya Amurka domin halartar wani taro kan zaman lafiya da tsaro a Washington DC.
Taron da hukumar zaman lafiya ta Amurka ta shirya, ya horas da gwamnonin kan hanyoyin magance matsalolin tsaro a shiyyar Arewacin Najeriya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng