Majalisa ta yi Bayani Kan Sayowa Shugaban Kasa da Mataimakinsa Sabon Jirgin Sama

Majalisa ta yi Bayani Kan Sayowa Shugaban Kasa da Mataimakinsa Sabon Jirgin Sama

  • Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio ya musanta labarin cewa sun amince da sayowa shugaban kasa da mataimakinsa sababbin jirage
  • Ya bayyana haka ne a Borno jim kadan bayan ziyarar ta'aziyya ga Sanata Tahir Munguno kan rasuwar mahaifinsa, inda ya ce sharri kawai aka yi masu
  • Rahotanni a baya sun bayyana cewa shugaban majalisar ya ce akwai bukatar a sayowa shugaba Tinubu da mataimakinsa, Shettima sabon jirgin sama

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Abuja- Shugaban majalisar dattawan kasar nan, Godswill Akpabio ya musanta cewa sun amince da sayowa shugaban kasa da mataimakinsa sabon jirgin sama.

Kara karanta wannan

Yan ta'adda sun mamaye fitaccen gari a Zamfara, dan majalisa ya nemi dauki

An samu rahotanni cewa majalisar ta sahale a sayowa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima sabon jirgi saboda nasu ya tsufa,

Godswill Obot Akpabio
Majalisa ta musanta amincewa da sayawa shugaban kasa da mataimakinsa sabon jirgi Hoto: Godswill Obot Akpabio
Asali: Facebook

Punch News ta wallafa cewa a martanin da majalisar ta yi, Sanata Akpabio ya ce babu kamshin cikin labarin cewa sun amince da sayo sababbin jirgin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Sharri aka yi mana," Godswill Akpabio

A sanarwar da hadimin shugaban majalisa kan yada labarai, Jackson Udom ya fitar, ya ce labarin cewa sun amince a sayo sababbin jiragen labarin karya ne.

Sanata Akpabio ya bayyana haka ne jim kadan ziyarar ta'aziyya ga Sanata Tahir Munguno kan rasuwar mahaifinsa, kamar yadda The Street Journal ta wallafa.

Sanata Akpabio ya kara da cewa lokacin da aka wallafa labarin, ba ya Najeriya, ya na Zanzibar a kasar Tanzania, saboda haka babu yadda za a yi a ce shi ya fada.

Kara karanta wannan

Mutuwar jami’in Kwastam: Shugaba Tinubu ya aikawa Iiyalin Marigayi Etop Essien saƙo

“ Ina so na karyata jita-jitar da ake yadawa da ku ka ji na cewa shugaban majalisa ya ce za a sayowa shugaban kasa da mataimakinsa sabon jirgi, duk da cewa 'yan Najeriya na cikin yunwa."

-Shugaban majalisa Godswill Akpabio

Akpabio ya ba wa 'yan Najeriya hakuri

A wani labarin kun ji cewa shugaban majalisa, Sanata Godswill Akpabio ya ba wa 'yan Najeriya hakuri kan halin matsin tattalin arziki da ake ciki.

Sanata Akpabio ya kuma dora laifin tattalin arziki da ake fuskanta kan tsare-tsaren da tsohon gwamnan babban bankin kasa (CBN), Godwin Emefiele.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.