Kungiyar Kwadago Ta Dauki Mataki Bayan Tinubu Ya Yi Biris da Maganar Ƙarin Albashi
- Kungiyar kwadago ta nuna rashin jin dadi kan yadda shugaban kasa Bola Tinubu ya yi watsi da maganar ƙarin albashin ma'aikata
- A sanadiyyar haka, 'yan kwadago sun dauki mataki domin duba abin da ya kamata su yi a gaba domin neman hakkin ma'aikata
- Kungiyar ta saka ran cewa a zaman majalisar zartarwar gwamnatin tarayya na jiya, shugaba Tinubu zai yi magana kan karin albashi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Nigeria - Rashin yin cikakken bayani da shugaban ƙasa Bola Tinubu ya yi kan karin albashi a zaman majalisar zartarwa ya fusata 'yan kwadago.
An saka rai a kan cewa Bola Tinubu zai bayyana matsayar gwamnatinsa kan karin albashi a jiya Talata.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa kungiyar kwadago ta dauki mataki domin duba yadda za ta fuskanci lamarin a gaba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Matakin da 'yan kwadago suka dauka
Kungiyoyin kwadago da suka haɗa da NLC da TUC za su yi taron gaggawa domin daukan mataki kan watsi da su da gwamnatin Bola Tinubu ta yi da maganar karin albashi.
Wani babban jami'in NLC ya tabbatar da cewa za a fara taron ne a yau Talata da misalin karfe 10:00 na safe domin daukan mataki, rahoton Daily Post.
Abin da ya faru a majalisar zartarwa
A jiya Talata ne shugaban kasa Bola Tinubu ya zauna da 'yan majalisar zartarwa domin tattauna matsalolin Najeriya.
Sai dai ministan sadarwa da wayar da kan al'umma, Muhammad Idris ya ce an tattauna dukkan abin da ya tara su sai dai magana kan karin albashi kawai.
Dalili daga maganar ƙarin albashi
Muhammad Idris ya bayyana cewa an daga magana kan karin albashi ne saboda Bola Tinubu yana bukatar neman shawari sosai kan lamarin.
Ministan ya kuma tabbatar da cewa gwamnatin tarayya ba za ta bayyana matsayarta ba har sai ta tattauna da gwamnonin jihohi kan lamarin.
'Yan kwadago sun yi kira ga Bola Tinubu
A wani rahoton, kun ji cewa kungiyar kwadago ta sake kira ga shugaban kasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu kan karin mafi ƙarancin albashi ga ma'aikata.
Wani dan kwamitin tattaunawa da gwamnatin Najeriya kan karin albashi, Adewale Adeyanju ne ya jaddada abin da suke so a biya ma'aikata.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng