Mutuwar Jami’in Kwastam: Shugaba Tinubu Ya Aikawa Iyalin Marigayi Etop Essien Saƙo

Mutuwar Jami’in Kwastam: Shugaba Tinubu Ya Aikawa Iyalin Marigayi Etop Essien Saƙo

  • Shugaba Bola Tinubu ya ce ya kaɗu da jin labarin mutuwar wani mataimakin shugaban hukumar Kwastam, DC Etop Essien.
  • Mai magana da yawun shugaban kasa, Ajuri Ngelale ne ya fitar da sakon ta'aziyyar Tinubu a ranar Talata, 25 ga watan Yuni
  • Mun ruwaito cewa DCG Etop ya yanke jiki ya fadi ne a yayin wani zaman ba da ba'asi kan gudanar da aiki a zauren Majalisar tarayya, Abuja

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya yi alhinin mutuwar mataimakin shugaban hukumar Kwastam, mai kula da sashen tattara haraji, DC Etop Andrew Essien.

Legit Hausa ta ruwaito cewa DC Essien ya yanke jiki ya fadi ne a zauren majalisar tarayya a lokacin da ya ke amsa tambayoyi daga kwamitin majalisar.

Kara karanta wannan

Babban jami'in hukumar Kwastam ya mutu ana tsakiyar zaman kwamitin Majalisa

Shugaba Tinubu ya aika muhimmin saƙo ga iyalan Etop Essien
Tinubu ya jajantawa kwastan bisa rasuwar mataimakin kwanturola, Etop Essien. Hoto: Uche Nnadozie
Asali: Facebook

Tinubu ya magantu kan mutuwar jami'in Kwastam

A cikin wata sanarwa da fadar shugaban kasa t fitar a X, an ce Bola Tinubu ya mika sakon ta'aziyya ga iyalan DCG Etop, yana mai jimamin wannan rashi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Haka zalika, shugaban kasar ya mika sakon ta'aziyya ga shugaban hukumar Kwastam na ƙasa, Bashir Adewale Adeniyi, da jami'an hukumar bisa rashin ma'aikacinsu.

Shugaban kasar na Najeriya ya yi addu'ar Allah ya jikan mamacin tare da ba iyalansa juriyar wannan babban rashi da suka yi.

Duba sanarwar a ƙasa:

Kwastam ta yi alhinin mutuwar DC Etop

A irin wannan yanayin ne shi ma shugaban hukumar Kwastam na ƙasa, Mista Adeniyi, a madadin ma'aikatan hukumar gaba daya ya mika sakon ta'aziyya ga iyalan DCG Etop.

Mista Adeniyi ya ce:

"Hukumar NCS ta kadu matuka da mutuwar wannan jajirtaccen jami'i. Muna a shirye wajen tallafawa iyalai da abokan aikin jami'in a yayin da suke makokin mutuwarsa."

Kara karanta wannan

IPMAN: Farashin litar man fetur ya kai N2,000 a jihar Arewa, an gano dalilin tashin

Duba sanarwar a kasa:

Abubuwa 3 game da Etop

A wani labarin, mun tattaro maku wasu muhimman abubuwa uku da ya kamata ku sani game da Etop Essien, jami'in Kwastam da ya mutu a zauren majalisar tarayya.

Daga cikin su akwai bayani kan yadda Etop Andrew Essien ya shafe shekaru sama da 30 yana aiki a hukumar NCS, kamar yadda rahoton hukumar ya nuna.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.