Mata Sun Fusata, Sun Rufe Kofar Shiga Filin Jirgin Sama Saboda Rashin Wuta a Ribas

Mata Sun Fusata, Sun Rufe Kofar Shiga Filin Jirgin Sama Saboda Rashin Wuta a Ribas

  • Ran mata a jihar Ribas ya baci biyo bayan rashin wuta da su ka ce ya addabi yankunansu, kan haka ne ma su ka tsunduma zanga-zanga domin nuna rashin din dadinsu
  • Matan da su ka fito daga yankin Ipo sun bayyana cewa wannan ba shi ne karon farko da su ka fito domin neman a agaza masu kan batun karancin wuta da su ke fuskanta ba
  • Amma sun shaidawa manema labarai cewa wannan karon da gaske su ke, domin sun fito da tukwanensu inda za su ci gaba da zama a wajen har sai an kawo masu dauki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Kara karanta wannan

Ruwa ya cinye wasu dalibai a hanyarsu ta dawo wa daga jarrabawa a Kaduna

Jihar Rivers- Wasu fusatattun mata sun shiga zanga-zanga domin nunawa mahukunta bacin ransu na rashin wuta da su ke fama da shi a yankunansu a jihar Ribas.

Matan sun rufe kofar shiga filin jirgin sama na Fatakwal da ke yankin Omagwa a jihar, inda su ka ce rashin kawo wuta a yankinsu ya jefa su cikin mawuyacin hali

Sir Siminalayi Fubara
Mata sun shiga zanga-zanga saboda rashin wuta a Ribas Hoto: Sir Siminalayi Fubara
Asali: Facebook

The Nation ta wallafa cewa matan sun fito da shirinsu, domin bayan rufe kofar sun dora tukwane inda su ka hau girke-girke da wakokin neman dauki kan rashin wutar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Masu zanga-zanga sun jawo cunkoso

Mata da ke zanga-zanga a jihar Ribas saboda matsalar rashin wuta sun jawo cunkosun ababen hawa, yayin da su ke hantarar fasinjojin da ke son shiga filin jirgin sama na Fatakwal.

Vanguard News ta wallafa cewa matan sun fito dauke da takardu tare da rera wakoki su na neman akawo masu dauki yankinsu na Ipo.

Kara karanta wannan

An shiga rudani, 'yan ta'adda sun lafta harajin wata wata a kan mazauna Binuwai

Wasu daga cikin matan sun shaidawa manema labarai cewa wannan ba shi ne karon farko da su ka nemi a kawo masu dauki ba.

Saboda haka ne suka fito da tukwanensu domin ba za su bar wajen ba sai an sama masu mafita.

Rashin wuta na kara kamari a Najeriya

A baya mun kawo labarin cewa mazauna Najeriya na cikin mawuyacin hali yayin da rashin wuta ke kara kamari a jihohin da ke kasar, duk da tsananin zafi da ake fuskanta.

An fara samun karuwar matsalar wuta ne tun bayan cire tallafi a bangaren, amma majalisa ta kira ministan lantarki na kasa, Adebayo Adelabu domin jin inda aka kwana.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Online view pixel