"Girma Ya Fadi": An Cafke Basarake da Kansilan APC Kan Zargin Satar Tiransifoma

"Girma Ya Fadi": An Cafke Basarake da Kansilan APC Kan Zargin Satar Tiransifoma

  • Dubun wasu masu girma a cikin al'umma ta cika bayan cafke su da satar tiransifomar wutar lantarki a jihar Gombe
  • Rundunar ƴan sanda ta yi nasarar cafke kansila da kuma dagacin kauyensu kan zargin sata da kuma siyar da tiransifoma
  • Legit Hausa ta ji ta bakin kakakin rudunar 'yan sanda a Gombe, ASP Buhari Abdullahi kan lamarin da halin da ake ciki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Gombe - Rundunar ƴan sanda a jihar Gombe ta cafke wani kansila kan zargin sace tiransifoman da ke raba wuta.

Ana zargin kansilan yankin Kumo ta Gabas a karamar hukumar Akko da ke jihar mai suna Abdullahi M Panda da sata.

Kara karanta wannan

Ruwa ya cinye wasu dalibai a hanyarsu ta dawo wa daga jarrabawa a Kaduna

Yan sanda sun kama basarake da kansila kan zargin satar tiransifoma
'Yan sanda a jihar Gombe sun kama wani kansila da basarake kan satar tiransifoma. Hoto: Gombe Police Command.
Asali: Facebook

Gombe: An cafke basarake, kansila da sata

Ƴan sandan sun cafke shi ne tare da Jauron Majidadi, Muhammad Majidadi da wani mutum daya bayan sun siyar da tiransifomar, kamar yadda Leadership ta wallafa faifan bidiyo a X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kakakin rundunar ’yan sanda a jihar, ASP Buhari Abdullahi ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce sun cafke su ne bayan samun bayanan sirri.

Buhari Abdullahi ya ce bayan gudanar da bincike, an gano sun siyar da tiransfomar kan kudi N1.5m ga wani mai suna Bello Ardo Kumo, cewar The Guardian.

Ya ce an karbo tiransifomar kuma da zarar an kammala bincike za a gurfanar da su a gaban kotu.

Martaninin wanda ake zargi da satar

Sai dai kansilan a bangarensa ya ce sun yi magana da dagacin kauyen kan lamarin inda ya bukaci su kawo batun a rubuce.

Kara karanta wannan

Yan sanda sun kama ƙasurgumin ɓarawo a Bauchi, ya sace N120m da kayayyaki rututu

Ya ce daga bisani sun kira mai saye ranar Juma’a inda ya ke kokarin daukar tiransifomar domin siyarwa ’yan sanda suka kama su.

Amma ya bukaci a kai su kotu domin a can ne zai shaidawa kotu abin da ya sani domin wanke kansa daga zargi.

Martanin kakakin 'yan sanda ga Legit Hausa

Legit Hausa ta ji ta bakin kakakin rudunar 'yan sanda a Gombe, ASP Buhari Abdullahi kan lamarin da halin da ake ciki.

ASP Buhari ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce yanzu haka sun mika wadanda ake zargi zuwa kotu domin daukar mataki.

Ya tabbatarwa da wakilin Legit Hausa cewa zai ba da karin bayani duk lokacin da aka samu ci gaba.

An kawo sabon tsarin almajirai a Gombe

A wani labarin, kun ji cewa Gwamnatin jihar Gombe ta amsa kiran da aka daɗe ana yi kan kawo gyara a harkar almajiranci a Najeriya.

Kara karanta wannan

Sarautar Kano: Abin da Sanusi II ya fadawa kungiyar mata masu tafsiri a fadarsa

Gwamnatin da dauki matakin samar da adadin almajirai a fadin jihar kan kokarin saka tsare-tsaren zamani a harkar almajiranci.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.