Ana Tsaka da Rigimar Sarauta, Sanusi II Ya Yi Biris da Kotu, Ya Tura Wakili Nassarawa

Ana Tsaka da Rigimar Sarauta, Sanusi II Ya Yi Biris da Kotu, Ya Tura Wakili Nassarawa

  • Ana tsaka da dambarwar sarautar jihar Kano, Muhammadu Sanusi II ya yi sabon nadin wakilinsa a Nassarawa
  • Sanusi II ya amince da tura Abdullahi Sarki (Jakadan Garko) domin ya zama wakilinsa a karamar hukumar Nassarawa
  • Abdullahi Sarki zai ci gaba da rike mukamin kafin Sarkin ya tura hikimi da zai jagoranci karamar hukumar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Duk da rigimar sarautar Kano da ake ciki, Muhammadu Sanusi II ya sake nadin mukamin a jihar.

Sarkin Kano, Sanusi II ya amince da tura Abdullahi Sarki (Jakadan Garko) domin rike karamar hukumar Nassarawa.

Sanusi II ya nada wakilinsa a Nassarawa a jihar Kano
Muhammadu Sanusi II ya tura wakili Nassarawa kafin nada sabon hakimi. Hoto: @masarautarkano.
Asali: Twitter

Sanusi II ya nada wakili a Nassarawa

Kara karanta wannan

Bidiyo: Muhammadu Sanusi II ya gana da fitaccen malamin Musulunci a fadar Sarkin Kano

Wannan na kunshe a cikin wata wallafa da Masarautar Kano ta yi a shafinta na X a daren jiya Litinin 24 ga watan Yunin 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanusi II ya nada Jakadan Garko wanda zai jagoranci karamar hukumar Nassarawa kafin ya tura sabon hakimi daga baya.

Jakadan Garko zai jagoranci karamar hukumar Nassarawa ne a matsayin wakilin Sarki na wani lokaci.

Nadin Abdullahi Sarki na zuwa ne yayin ake ci gaba da dambarwa kan ainihin sahihin Sarki a jihar bayan hukuncin kotu.

Kano: Hukuncin kotu ya jawo rudani

Hukuncin kotun ya jawo rudani inda wasu ke ganin akwai rikitarwa a cikin hukuncin Babbar Kotun Tarayya.

Sai dai wasu lauyoyi sun tabbatar da cewa komai a fayyace ya ke kan hukuncin kotun babu matsala da rikitarwa a ciki.

Duk da haka wasu manyan lauyoyi sun ki cewa uffan game da matakin da kotun ta dauka saboda suna zargin an saɓa dokoki yayin yanke hukuncin a Kano.

Kara karanta wannan

Sanusi II Vs Bayero: Manazarci ya hango makomar sarautar Kano bayan hukuncin kotu

Sheikh Dokoro ya magantu kan sarautar Kano

A wani labarin, kun ji cewa Sheikh Muhammad Adamu Dokoro ya magantu kan rigimar sarautar jihar Kano da ake ciki yanzu.

Shehin malamin ya shawarci Abba Kabir da Sanusi II da kuma Aminu Ado Bayero su tabbatar da cewa domin Allah suke wannan rigima.

Malamin ya ce idan har domin daukar fansa ko gabar siyasa suke yi to tabbas Allah zai wargaza su cikin sauki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.