Duk da Jimamin Rasuwar Surukarsa, Kashim Shettima ya Tura Sako kan Tsige Sarkin Musulmi

Duk da Jimamin Rasuwar Surukarsa, Kashim Shettima ya Tura Sako kan Tsige Sarkin Musulmi

  • Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya yi kakkausan suka kan rahoton kokarin da gwamnatin jihar Sokoto ke yi na tsige Sarkin musulmi daga mukaminsa'
  • A safiyar yau ne rahotanni su ka karade jaridu bayan kungiyar kare hakkin musulmi ta Najeriya (MURIC) ta bankado zancen cire mai alfarma Abubakar Muhammad Sa'ad III
  • Kashim Shettima ya bayyana cewa tilas ne a kare martabar Sarkin musulmi, kuma abu ne wanda bai kamata ba gwamnatin Sokoto ta yi tunanin cire shi daga mukaminsa

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Kaduna-Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya gargadi gwamnatin jihar Sokoto kan yunkurin da ta ke yi na cire sarkin musulmi, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar daga mukaminsa.

Kara karanta wannan

Gwamna ya dauki tsattsauran mataki kan masallatai da coci a Plateau, ya kakaba doka

A safiyar yau ne kungiyar da ke rajin kare hakkin musulmi ta Najeriya (MURIC) ce ta yi kururuwar cewa ta gano makarkashiyar cire sarkin musulmin.

Kashim Shettima
Mataimakin shugaban kasa ya yi gargadi kan yunkurin cire sarkin musulmi Hoto: Kashim Shettima
Asali: Facebook

Daily Trust ta wallafa cewa da ya ke martani kan labarin, mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya ce Sarkin Musulmin ba sarki ne kawai a Sokoto ba, ya wuce haka.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Sultan sarkin duk muslmin Najeriya ne," Shettima

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya magantu kan yunkurin cire Sarkin musulmi, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III yayin taron tsaro a Katsina.

Vanguard News ta wallafa cewa kimar da Sarkin Musulmi ke da ita ya wuce a ce za a tumbuke rawaninsa a kasar nan, inda ya ce Sarki ne na musulmin kasa.

“Kuma zuwa ga mataimakin gwamnan Sokoto, ina da sako gare ka, e, Sultan Sultan ne a Sokoto, amma ya wuce haka; wakili ne na ra'ayi, cibiya ce da dukkanin musulmin kasar ya kamata su kare martabarsa."

Kara karanta wannan

Matsin rayuwa: Tinubu ya shawarci 'yan Najeriya kan yadda za su samu abinci cikin sauki

- Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima

"Ana shirin tsige Sarkin musulmi," MURIC

A wani labarin kun ji cewa kungiyar da ke rajin kare hakkin musulmin Najeriya (MURIC) ta yi kwaroroton cewa gwamnatin jihar Sokoto na yunkurin cire sarkin musulmi daga mukaminsa.

Shugaban kungiyar, Ishaq Akintola ne ya yi gargadin ta cikin sanarwar da ya fitar, inda ya gargadi gwamnatin jihar da cewa bakin rijiya ba wurin wasan yaro ba ne.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.