'Yan Sanda Sun Bankado Sababbin Dabarun Kwacen Babura, An Fargar da Matuka

'Yan Sanda Sun Bankado Sababbin Dabarun Kwacen Babura, An Fargar da Matuka

  • Rundunar 'yan sandan Osun ta gargadi masu sana'ar tuka babura da su bi a hankali domin an gano sababbin dabarun kwacen abin hawan da barayi ke yi a jihar
  • Jami'in hulda da jama'a na rundunar a jihar, SP Yemisi Opalola ya shaidawa manema labarai cewa gargadin ya zama dole saboda karuwar rahotannin satar babura
  • SP Yemisi Opalola ya bayyana cewa yanzu haka an gano barayin su na tare masu babura, sannan su ja su lungu inda a nan ne su ke yin kwacen cikin ruwan sanyi

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Osun- Karuwar rahotannin kwacen babura a jihar Osun ya tilasta rundunar 'yan sandan daukar matakin sanar da jama'a sabon dabarar barayin da ke kwacen.

Kara karanta wannan

Kwalara na kisa a awanni, gwamnatin Kano ta yi gargadin amfani da ruwan sama

Rundunar ta gargadi masu sana'ar cewa an gano miyagun na tare masu babura, sai su ja su lungu inda a nan ne su ke tilasta masu rabuwa da babura ba tare da an gansu ba.

Nigeria Police Force
Rundunar 'yan sanda ta gargadi masu babura kan dabarun kwace da aka bullo da shi Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

Vanguard News ta wallafa cewa jami'in hulda da jama'a na rundunar, SP Yemisi Opalola ya gargadi masu babura da su sanya idanu kan irin fasinjojin da su ke dauka.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Osun: An samu karuwar satar babur

Jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan Osun ta bayyana cewa an samu karuwar rahotannin kwacen babura a fadin jihar.

Kakakin ya gargadi masu sana'ar tuka babura da su lura da fasinjojin da ke neman a kai su loko musamman idan sawu ya dauke, domin a nan aka fi yin ta'asar.

Peoples Gazzette ta wallafa cewa an gano barayin da ke badda-bami a matsayin fasinjoji, su na yiwa masu baburan tayin kudin da ba su iya kin daukarsu.

Kara karanta wannan

Yadda kwankwaɗar kunun aya ya hallaka mutane 24, Gwamna ya dauki mataki mai tsauri

An shiga damuwa bayan kashe dan sanda

A wani labarin kun ji cewa an shiga zaman dar-dar bayan wasu sojojin ruwa sun yi sanadiyyar mutuwar jami'in dan sanda a unguwar Okokomaiko da ke jihar Legas.

Jami'an hulda da jama'a na rundunar, Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da rasuwar jami'in mai matsayin sufeto inda ya ce ya yanke jiki ya fadi, kuma an tabbatar da rasuwarsa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.