Rusa Fadar Nasarawa: Gwamnatin Abba Ta Ba Aminu Bayero Sabon Umarni a Kano

Rusa Fadar Nasarawa: Gwamnatin Abba Ta Ba Aminu Bayero Sabon Umarni a Kano

  • An umurci abokin hamayyar Muhammadu Sanusi II, Aminu Ado Bayero da ya fice daga karamar fadar Nasarawa cikin gaggawa
  • Gwamnatin Kano karkashin jagorancin Abba Yusuf ta bayar da umarnin bayan kotu ta bayyana tsige Bayero a matsayin laifi
  • A hannu daya kuma, ‘yan sanda a Kano sun mamaye fadar Sarkin Kano tare da korar 'yan taurin da aka ce suna gadin Sanusi II

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Kano - Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya ba tsohon Sarkin Kano, Aminu Bayero umarnin barin fadar Nasarawa inda yake zama ba tare da bata lokaci ba.

Gwamnan Abba Yusuf ya ce yana so ya rushe wasu bangarori na fadar ne domin yin gyare-gyare da kuma yin sabon gini.

Kara karanta wannan

Babbar kotu ta dauki mataki a shari'ar tsige Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero

Gwamnatin Kano ta ba Aminu Bayero sabon umarni
Sarkin Kano na 15, Aminu Bayero da Gwamnan Kano Abba Yusuf. Hoto: Aminu Ado Bayero, Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Abba ya ba Aminu Bayero sabon umarni

A wani rahoto da jaridar The Nation ta fitar, an ce gwamnatin Kano ta nuna takaicinta kan yadda har yanzu Aminu Bayero bai fice daga fadar ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A sanarwar da gwamnatin ta fitar ranar Lahadi, 23 ga watan Yuni, an nemi Sarkin Kano na 15 da ya bar fadar cikin gaggawa domin kare martabarsa.

N99.9m: An ware kudin gyara fadar Nasarawa

Jaridar New Telegraph ta ruwaito cewa gwamnatin Kano ta kuma shawarci Aminu Bayero da ya fice daga fadar saboda kare lafiyarsa da kuma gujewa shan kunya.

A ranar Asabar ne gwamna Abba Yusuf ya bayar da umarnin fitar da Naira miliyan 99.9 domin gini da gyara fadar Nasarawa.

Amincewa da fitar da wannan kudin ya bidiyo bayan wani taron majalisar zartarwar jihar da ya gudana a ranar Asabar din bisa jagorancin gwamnan.

Kara karanta wannan

Sanusi II Vs Bayero: Manazarci ya hango makomar sarautar Kano bayan hukuncin kotu

'Yan sandan Kano sun mamaye fadar sarki

Tun da farko dai, mun ruwaito cewa jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Kano sun kai mamaya fadar sarki tare da tarwatsa 'yan taurin da ke kare Muhammadu Sanusi II.

Ana zargin mamayar ‘yan sandan wani mataki ne na tabbatar da tsaron babban gidan sarautar a wani shiri na mayar da Aminu Bayero, tsohon Sarkin Kano na 15 cikin fadar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.