Sarautar Kano: Babban Malamin Musulunci Ya Ba Gwamna Abba, Sanusi II da Aminu Ado Shawara
- Fitaccen malamin addinin Musulunci a jihar Gombe, Sheikh Muhammad Adamu Dokoro ya yi martani kan dambarwar sarautar Kano
- Shehin malamin ya shawarci dukan wadanda ke cikin rigimar da gwamnan jihar da su tabbatar domin Allah suke yi
- Ya ce duk wanda ya ke yin wannan fafatawa ba saboda Allah ba sai domin daukar fansa ko gabar siyasa to ba zai ga da kyau ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Yayin da ake dambarwa kan sarautar Kano, fitaccen malamin Musulunci a Gombe, Sheikh Adamu Dokoro ya magantu.
Dokoro ya bukaci masu neman sarauta da gwamnan jihar da sauran talakawan gari da su rinƙa yin abu domin Allah idan ana neman taimakonsa.
Malamin Musulunci ya magantu kan sarautar Kano
Shehin malamin ya bayyana haka ne a cikin wani faifan bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Facebook kan rigimar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya shawarci Gwamnan Abba Kabir da kada ya saka siyasa ko niyyar muzanta wani ko zugin wani domin aiwatar da abin da bai dace ba.
Har ila yau, Dokoro ya bukaci Sanusi II da ya tabbatar abin da yake yi domin Allah ne ba wai kawai ramuwar gayya kan abin da ya faru da shi a baya ba.
Daga bisani, malamin ya ce idan Aminu Ado dagewar da ya ke yi ba domin Allah ba ne sai domin don zuciya to ba zai ga da kyau ba shima.
Kano: Malamin ya shawarce su gaba daya
Dokoro ya shawarce su gaba daya da su tabbatar domin Allah suke wannan dambarwa idan kuma ba haka ba ne to Allah zai tarwatsa su gaba daya.
A karshe, ya yi addu'ar Ubangiji ya kawo saukin lamarin ba tare da zubar da jini ba inda ya ce zunubin na kan wadanda suka jawo.
Lauyoyi sun bambanta kan rigimar sarautar Kano
A wani labarin, kun ji cewa Yayin da ake ci gaba dambarwa kan sarautar Kano, wasu manyan lauyoyi sun ki cewa komai kan lamarin.
Daga cikin wadanda suka ki yin martani akwai Samuel Jibrin Okutepa SAN da Dakta Richard Oma Ahunauogho SAN da Israel Olorundare SAN.
Asali: Legit.ng