Allahu Akbar: An Yi Jana’izar Mahaifin Sanatan Arewa, Shettima da Sanatoci Sun Halarta

Allahu Akbar: An Yi Jana’izar Mahaifin Sanatan Arewa, Shettima da Sanatoci Sun Halarta

  • Mun samu labarin rasuwar Alhaji Tijjani Muhammad, mahaifi ga sanatan mazabar Borno ta Arewa, Sanata Mohammed Tahir Munguno
  • Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya jagoranci tawagar gwamnatin tarayya zuwa jana'izar Alhaji Tijjani Muhammad a Borno
  • An dai bayyana marigayi Alhaji Tijjani a matsayin mutumin kirki wanda ya rasu yana da shekara 95 kuma ya bar ƴaƴa 17 a raye

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya jagoranci tawagar gwamnatin tarayya zuwa jana'izar Alhaji Tijjani Muhammad, mahaifin sanatan Borno ta Arewa, Mohammed Tahir Munguno.

An ruwaito cewa marigayi Alhaji Muhammad, ya rasu ne a daren ranar Asabar a asibitin koyarwa na jami'ar Maiduguri bayan doguwar jinya, yana da shekaru 95.

Kara karanta wannan

Zaben 2027: Atiku ya bayyana mafita 1 game da rikicin da ya mamaye PDP a Katsina

An gudanar da jana'izar mahaifin Sanata Mohammed Tahir Munguno
Shettima ya jagoranci tawagar gwamnatin tarayya zuwa jana'izar mahaifin Sanata Munguno. Hoto: @KashimSM
Asali: Twitter

Kamar yadda Kashim Shettima ya wallafa a shafinsa na X a ranar Lahadi, babban limamin Borno, Mamman Shettima Saleh ne ya jagoranci Sallar jana'izar a tsohon gidan Sanata Munguno.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daga cikin wadanda suka halarci jana'izar akwai mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin, Sanata Ali Ndume da ministan noma, Abubakar Kyari.

Sauran sun hada da ministan cikin gida kan ci gaba ƙarafa, Uba Maigari Ahmadu, mukaddashin gwamnan Borno, Dr. Usman Kadafur da dai sauran su.

Duba hotunan jana'izar da ta'aziyyar a nan ƙasa:

Sanata Barau ya miƙa saƙon ta'aziyya

Sanata Barau Jibrin, ya wallafa a shafinsa na X cewa:

"InnalilLahi wa inna ilaihi raji'un.

"A yau na kasance a Maiduguri, babban birnin jihar Borno inda na halarci jana'izar Alhaji Tijjani Muhammad, mahaifin abokinmu, Sanata Tahir Munguno."

Kara karanta wannan

"Atiku na shirya wani abu": 'Dan takaran PDP ya ziyarci Buhari a Daura

Kalli saƙon sanatan a nan ƙasa:

"Alhaji Tijjani mutumin ƙwarai ne" - Ali

Tun da fari, wani ma'abocin shafin Facebook, Muhammad Umar B. Ali ne ya sanar da rasuwar Alhaji Tijjani Muhammad a jiya Asabar, 22 ga watan Yuni.

Umar B. Ali ya ce Alhaji Tijjani ya kasance ɗan kasuwa na ƙasa da ƙasa, wanda ya kasance mutumin ƙwarai, abin koyi ga jama'a.

Ya ce Alhaji Tijjani ya rasu ya bar ƴaƴa 17, ciki har da Sanata Munguno, da Injiniya Usman, shugaban kungiyar injiniyoyi ta Borno, da Barista Ibrahim, wanda ya assasa cambar lauyoyi ta Munguno, da dai sauran su.

Duba hoton marigayi Alhaji Tijjani Muhammad a ƙasa:

Mahaifiyar Pele ta riga mu gidan gaskiya

A wani labarin, mun ruwaito cewa, mahaifiyar fitaccen dan wasan kwallon kafa na Brazil, Pele, ta mutu a kasar Brazil tana da shekaru 101 bayan fama da jinya.

Wata sanarwa da hukumar kwallon kafar Brazil ta fitar ta ce Celeste Arantes ta yi jinyar kwana takwas a asibiti kafin mutuwarta a ranar Juma'a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.