Yanzu-yanzu: Allah ya yi wa Mahaifin Sanatan Nijeriya Rasuwa

Yanzu-yanzu: Allah ya yi wa Mahaifin Sanatan Nijeriya Rasuwa

  • A yau ne aka tashi da jimamin rasuwar mahaifin daya daga cikin sanatocin Nijeriya
  • Alhaji Ali Buba Ndume wanda mahaifi ne wurin Sanata mai wakiltar Borno sanata Ali Ndume ya rigamu gidan gaskiya
  • za'ayi jana'izar sa da karfe 4 na yamma a Maiduguri jihar Borno

Alhaji Ali Buba Ndume, Mahaifin sanata mai wakiltar Borno ta kudu a majalisar dattawa, Mohammed Ali Ndume ya rigamu gidan gaskiya.

Sanatan da kanshi ya bayyana haka a wani jawabi da ya rabawa manema labarai a Abuja ranar Talata.

Ya kara da bayyana cewa za'a yi jana'izar mahaifin nashi yau Talata a Maiduguri jihar Borno.

Ali Ndume
Yanzu-yanzu: Allah ya yi wa Mahaifin Sanatan Nijeriya Rasuwa
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Jawabin yace "Muna bakin cikin sanar da ku cewa Allah ya yiwa Alhaji Ali Buba Ndume , Mahaifin Sanata Mohammed Ali Ndume rasuwa. Ya rasu da safiyar yau a Maiduguri.

Kara karanta wannan

Rundunar yan sanda ta ayyana neman shugaban yan bindiga, Ado Aleru, ruwa a jallo

"Allah ya jikanshi ya ba iyalanshi hakurin rashin da suka yi.

"za'a yi jana'izar sa da karfe 4 na yamma a gidan Sanata Mohammed Ali Ndume a Damboa kusa da NTA a Maiduguri."

Daman majalisar ta dage zamanta na ranar talata zuwa ranar Laraba saboda girmama daya daga cikin mamban majalisar wakilai, Jude Ise-Idehen da ya rasu kwanan nan.

Mamban ya kasance mai wakiltar Egor/Ikpoba Okha a majalisar jihar Edo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel