"Mun Yi Rabo Ubangiji Na Tare da Tinubu": Malamin Addini Ya Fadi Abin da Zai Faru da Najeriya

"Mun Yi Rabo Ubangiji Na Tare da Tinubu": Malamin Addini Ya Fadi Abin da Zai Faru da Najeriya

  • Fitaccen Fasto a Najeriya ta tabbatar da cewa Najeriya za ta gyaru nan ba da jimawa ba ganin yadda lamura suka
  • Fasto Peter Adebisi Abiola ya ce tuni Najeriya da ta ruguje idan ubangji bai tare da Shugaba Bola Tinubu a halin yanzu
  • Adebisi ya koka kan yadda ƴan siyasa ke yaudarar mutane da kudi domin su zabe su inda ya ce hakan abin takaici ne

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Fitaccen Fasto a Najeriya, Peter Abiola Adebisi ya magantu kan salon mulkin Shugaba Bola Tinubu.

Faston ya ce Ubangiji yana tare da Tinubu shiyasa har yanzu kasar ba ta ruguje ba take tsaye da kakafunta.

Kara karanta wannan

Sarautar Kano: Abba Kabir ya magantu kan mutuncin Aminu Ado, ya fadi masu zuga shi

Malamin addini ya magantu kan salon mulkin Tinubu
Fasto Adebisi Abiola ya ce Najeriya ta yi rabo Ubangiji na tare da Bola Tinubu. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Fasto ya ce ubangji na son Tinubu

Malamin addinin ya bayyana haka ne yayin hira da jaridar The Nation a jiya Asabar 22 ga watan Yunin 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Peter wanda shi ne shugaban cocin Christ Miracle Church Mission ya ce komai zai daidaita a Najeriya.

"Muna godiya ga Ubangiji, idan da ba ya tare da Bola Tinubu da yanzu kasar Najeriya ta ruguje."
"Akwai abubuwa da dama da kuma shaidar cewa Ubangiji yana tare da Tinubu."
"Tun da kuwa Ubangiji yana tare da shi to tabbas komai zai daidaita a Najeriya ya zama tarihi."

- Peter Adebisi Abiola

Faston ya magantu kan siyan kuri'u a zaɓe

Malamin ya koka kan yadda wasu ke karbar kudi domin yin zaɓe daga hannun ƴan siyasa inda ya ce hakan siyar da ƴanci ne.

Faston ya ce shugabanni nagari za su zama jagorori ne idan har ƴan Najeriya suka bar siyar da ƴancinsu lokacin zaɓe.

Kara karanta wannan

Kano: Farfesa ya fadi yadda Abba zai yi nasara, ya magantu kan rusa fadar Nassarawa

Kwankwaso ya soki shugabanni kan siyan kuri'a

A wani labarin mai kama da wannan, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya koka kan yadda ake yaudarar mutane wajen siyan kuri'unsu a zabe.

Kwankwaso ya ce hakan shi ke sanya mutane zaben azzaluman shugabannin da za su ci gaba azabtar da jama'a a Najeriya.

Ya kuma ce babban matsalolin da ake fuskanta a Arewacin Najeriya rashin shugabanci ne nagari da sauran matsaloli.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.