Ta'addanci a Najeriya: Za a Gudanar da Gagarumin Taro Irinsa na Farko a Arewa

Ta'addanci a Najeriya: Za a Gudanar da Gagarumin Taro Irinsa na Farko a Arewa

  • Damuwa kan yadda matsalar tsaro ta hana jama'ar Arewacin Najeriya sakat, za a gudanar da wani babban taron masu ruwa da tsaki a jihar Katsina ranar Asabar
  • Wannan shi ne karon farko da za a gudanar da babban taro irin wannan a Arewa duk da kalubalen rashin tsaro da ya addabi al'umar yankin na tsawon shekaru
  • Gwamnatin jihar Katsina ta bakin kwamishinan yada labarai da al'adu, Dr Bala Salisu Zango ya bayyana cewa gwamnatinsu ta kammala shirin gudanar da taron

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Katsina - Kungiyar gwamnonin Arewa maso yamma a Najeriya da hadin gwiwar sashen kula da jama'a na majalisar dinkin duniya (UNDP) sun shirya tattaunawa kan shawo kan matsalar tsaro.

Kara karanta wannan

Matsin rayuwa: Tinubu ya shawarci 'yan Najeriya kan yadda za su samu abinci cikin sauki

Za a gudanar da taron tsaro a Arewa maso Yamma karo na farko a jihar Katsina domin lalubo hanyoyin da za a bi wajen dakile ta'addanci a yankin.

Dr. Dikko Umaru Radda
Gwamnoni, UNDP za su gudanar da babban taro kan tsaro a Katsina Hoto: Dr. Dikko Umaru Radda
Asali: Facebook

A wani labari da Daily Trust ta wallafa, za a gudanar da taron daga ranar Litinin, 24 Yuni 2024, zuwa Talata 25 Yuni, 2024 da zummar samun sauki a yankin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me za a gudanar yayin taron?

Ana sa ran shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu zai yi jawabi a taron wanda zai zama karon farko da zai ziyarci jihar tsohon shugaba Buhari tun bayan kama mulki.

Peoples Gazzette ta wallafa cewa kwamishinan yada labarai da al'adu na Katsina, Dr Bala Salisu Zango ya ce sun kammala shirin gudanar da taron.

Ya ce wannan ne karon farko da gwamnonin za su hadu a irin wannan muhimmin taro domin gano yadda za a kakkabe rashin tsaro a jihohin Arewa maso Yamma.

Kara karanta wannan

Kwalara na kisa a awanni, gwamnatin Kano ta yi gargadin amfani da ruwan sama

"Akwai hannun manya cikin rashin tsaro," Radda

A baya mun kawo labarin cewa gwamnan jihar Katsina, Umaru Dikko Radda ya zargi shugabanni da ma'aikatan gwamnati da hannu cikin rashin tsaro.

Gwamnan ya ce sun mayar da rashin tsaro da garkuwa da mutane sana'a, shi yasa har yanzu ake fuskantar kalubale wajen magance matsalar a jiharsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.