'Yan Bindiga Sun Fakaici Ƴan Kauye da Tsakar Dare, Sun Yi Ta'asa da Kone Kone a Katsina

'Yan Bindiga Sun Fakaici Ƴan Kauye da Tsakar Dare, Sun Yi Ta'asa da Kone Kone a Katsina

  • Rundunar ƴan sanda ta tabbatar da mummunan hari da ƴan bindiga suka kai a karamar hukumar Danmusa da ke jihar Katsina
  • Maharan sun kai harin ne a daren jiya Asabar 22 ga watan Yunin 2024 inda suka hallaka mutane bakwai
  • Kakakin rundunar ƴan sanda a jihar, ASP Abubakar Sadiq ya tabbatar da cewa an kaddamar da bincike kan lamarin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Katsina - Ƴan bindiga sun sake kai hari kauyen Mai Dabino da ke ƙaramar hukumar Danmusa a jihar Katsina.

Maharan sun kai farmakin ne da daren jiya Asabar 22 ga watan Yunin 2024 a kauyen bayan harbe-harbe inda suka hallaka mutane bakwai.

Kara karanta wannan

An shiga ɗimuwa bayan wasu miyagu sun hallaka Birgediya-janar na soja a Abuja

'Yan bindiga sun yi ta'asa a jihar Katsina da tsakar dare
'Yan bindiga sun tafka barna a jihar Katsina tare da hallaka mutane 7.
Asali: Original

Katsina: Ƴan bindiga sun hallaka mutane 7

Wani shaidan gani da ido ya tabbatarwa Channels TV cewa ya gano maharan sun sace mutane da dama mafi yawansu mata da yara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce maharan sun kai harin ne da misalin karfe 10.00 na dare inda suka shafe awanni uku suna cin karensu babu babbaka.

Har ila yau, ya ce maharan sun kona shaguna da gidaje da kuma motoci na miliyoyin kudi yayin harin, cewar Punch.

Rundunar ƴan sanda ta dauki mataki kan harin

Kakakin rundunar yan sanda, ASP Abubakar Sadiq ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce an kaddamar da fara bincike.

Ya ce sun samu rahoton harin inda maharan suka zo da muggan makamai tare da hallaka mutane bakwai.

"Jiya Asabar 22 ga watan Yunin 2024, ƴan bindiga dauke da muggan makamai sun kai hari kauyen Mai Dabino da ke karamar hukumar Danmusa."

Kara karanta wannan

Yadda kwankwaɗar kunun aya ya hallaka mutane 24, Gwamna ya dauki mataki mai tsauri

- ASP Abubakar Sadiq

Ƴan bindiga sun hallaka babban soja

A wani labarin, kun ji cewa wasu yan bindiga sun hallaka Birgediya-janar mai ritaya a birnin Abuja a daren jiya Asabar 22 ga watan Yunin 2024.

Maharan sun farmaki gidan tsohon sojan ne da misalin karfe 3.00 na tsakar dare inda suka yi ajalinsa nan take.

Kakakin rundunar ƴan sanda a birnin, Adeh Josephine ta tabbatar da faruwar lamarin a yau Lahadi inda ta ce an fara bincike.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.