Sarautar Kano: Kungiyar Lauyoyin Arewa Ta Fadi Sahihin Sarkin Kano Bayan Yanke Hukunci
- Kungiyar lauyoyi ta NCNLPIA ta yi martani kan hukunci kotu game da dambarwar sarautar Kano
- Kungiyar ta lauyoyin Arewacin Najeriya ta yabawa kotu bayan hukuncin da ta yi a jihar kan rigimar sarautar
- Ta tabbatar da cewa hukuncin ya tabbatar da Aminu Ado Bayero a matsayin sarkin Kano kamar yadda ake muradi
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Kungiyar lauyoyi a Arewacin Najeriya (NCNLPIA) ta sake magana kan dambarwar sarautar Kano.
Kungiyar ta ce Aminu Ado Bayero shi ne Sarkin Kano a yanzu bayan hukuncin Babbar Kotun Tarayya.
Kano: Lauyoyi sun yabawa hukuncin kotu
Lauyoyin suka ce hukuncin ya tabbatar da saɓa doka da Gwamna Abba Kabir ya yi wajen rusa masarautun jihar guda biyar, cewar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban kungiyar, Barista Napoleon Otache ya yabawa kotu kan hukuncin da ta yi na adalci.
"Rusa matakan Gwamna Abba Kabir da kotun ta yi ya tabbatar da cewa a yanzu kotu ne gatan talaka a Najeriya."
"Muradun al'umma sune kan gaba da komai kuma wadanda ke da gaskiya ba su bukatar tayar da hankula domin tabbatar da ƴancinsu."
- Napoleon Otache
Lauyoyi sun ba Abba Kabir shawara
Har ila yau, kungiyar ta bukaci Abba Kabir ya ba Aminu Ado Bayero hakuri kan irin cin mutunci da kuma wulakanci da ya yi masa.
Kungiyar ta kuma shawarci Abba Kabir ya tabbatar da yin biyayya ga hukuncin domin samun zaman lafiya a jihar.
Hakan ya biyo bayan hukuncin Babbar kotun Tarayya a rigimar sarautar Kano da aka kwashe makwanni amma yi.
Abba Hikima ya magantu kan sahihin Sarki
A wani labarin, kun ji cewa lauya Abba Hikima ya magantu kan sahihin Sarkin Kano yayin da ake ci gaba da dambarwar.
Hikima ya ce Aminu Ado Bayero shi ne Sarkin Kano idan aka yi duba a mahangar shari'a da dokar kasa bayan hukuncin kotu.
Wannan na zuwa ne bayan yanke hukunci da Babbar Kotun Tarayya ta yi a jihar kan rigimar sarautar jihar tsakanin Muhammadu Sanusi II da Aminu Ado Bayero.
Asali: Legit.ng