Sanusi II vs Aminu Ado: Babban Lauya Ya Bayyana Sahihin Sarkin Kano

Sanusi II vs Aminu Ado: Babban Lauya Ya Bayyana Sahihin Sarkin Kano

  • Wani lauya mazaunin Kano Umar Sa’ad Hassan ya fassara hukuncin da babbar kotun tarayya ta yanke kan rikicin masarautar Kano
  • Umar Hassan ya ce yayin da gwamnatin jihar Kano da ɓangaren Aminu Ado Bayero ke bayar da ma'ana daban-daban, hukuncin yana nufin Muhammadu Sanusi II ya daina zama Sarkin Kano
  • A wata tattaunawa ta musamman da Legit.ng lauyan ya yi bayanin cewa matakin da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ɗauka na dawo da Sanusi II a matsayin Sarki bai inganta ba saboda ya yi ne bayan kotu ta ba da umarni

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Ƙwararren mai sasantawa kuma mai shiga tsakani, Umar Sa’ad Hassan, ya yi magana kan hukuncin babbar kotun tarayya kan rikicin masarautar Kano.

Kara karanta wannan

Rikicin sarauta: Gwamna Abba na cikin Matsala, an bayyana sahihin Sarkin Kano

Lauyan ya ce hukuncin da babbar kotun tarayya ta yanke kan rikicin masarautar Kano na nufin Muhammadu Sanusi II ba shi ba ne Sarkin Kano.

Lauya ya fassara hukuncin kotu kan rikicin sarautar Kano
Lauya ya ce Sanusi II ba shi ba ne Sarkin Kano Hoto: Sanusi Lamido Sanusi, Totori Master
Asali: Twitter

Umar Hassan ya bayyana cewa hukuncin da mai shari’a Muhammad Liman ya yanke ya amince da dokar masarautun Kano ta 2024 a matsayin wacce ta dace amma ba matakin da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ɗauka ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana haka ne a wata tattaunawa ta musamman da Legit.ng ta yi da shi a ranar Asabar, 22 ga watan Yuni.

Lauya ya fassara hukuncin kotu kan Sarkin Kano

Lauyan da ke zaune a Kano ya bayyana cewa umarnin da babbar kotun tarayya ta bayar a ranar 23 ga watan Mayu ya warware dukkanin ayyukan da Gwamna Abba Yusuf ya yi a lokacin mayar da Sarki Sanusi II kan kujerarsa.

Kara karanta wannan

Sanusi II vs Aminu: Hadimin gwamna da fitaccen lauya sun samu saɓani kan hukuncin kotu

Umar Hassan ya ci gaba da cewa gwamnan zai iya aiwatar da dokar ne kawai bayan kotu ta ɗage wannan umarni.

"Dukkanin ɓangarorin biyu suna ba da fassarori daban-daban amma ni fahimtar da nake da ita ita ce dokar tana da inganci amma duk ayyukan da gwamnati ta yi bayan umarnin da aka bayar a ranar 23 ga Mayu ba su inganta ba."
"Hakan na nufin Muhammad Sanusi II zai daina zama Sarkin Kano."

- Umar Sa'ad Hassan

Batun hukuncin kotu kan Sarkin Kano

A wani labarin kuma, kun ji cewa Law Mefor, fitaccen mai sharhi kan al'amuran yau da kullumal ya ce gwamnatin jihar Kano ba ta ikon sauya hukuncin da kotu ta yanke.

Mefor ya bayyana cewa idan gwamnatin Abba Kabir tana da ja da hukuncin babbar kotun tarayya, kamata ya yi ta ɗaukaka ƙara ba wai ta take umarnin doka ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng