An Shiga Ɗimuwa Bayan Wasu Miyagu Sun Hallaka Birgediya Janar a Abuja

An Shiga Ɗimuwa Bayan Wasu Miyagu Sun Hallaka Birgediya Janar a Abuja

  • Wasu da ake zargin ƴan fashi sun yi ajalin Burgediya-janar mai ritaya a birnin Abuja da tsakar daren yau Lahadi
  • Maharan sun yi ajalin Uwem Harold Udokwe a cikin gidansa da misalin karfe 3.00 na dare bayan hari da suka kai
  • Kakakin rundunar ƴan sanda a birnin Abuja, SP Adeh Josephine ta tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Ana zargin ƴan fashi sun hallaka wani Burgediya-janar na sojoji mai ritaya a birnin Abuja.

Marigayin mai suna Uwem Harold Udokwe ya gamu da ajalinsa ne bayan ƴan fashin sun shiga gidansa tare da hallaka shi da misalin karfe 3.00 na dare.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun kashe ƴan bindiga 220, sun ƙwamuso wasu sama da 300 a Najeriya

'Yan fashi sun yi ajalin Burgediya-janar mai ritaya a Abuja
Wasu ƴan fashi sun shiga gidan Burgediya-janar mai ritaya inda suka yi ajalinsa a Abuja. Hoto: Nigeria Police Force.
Asali: Facebook

Ƴan fashi sun hallaka Janar din soja

Kwamishinan ƴan sanda a birnin Abuja, Benneth Igweh ya tabbatar da kisan tsohon soja wanda ya yi ritaya kamar yadda rundunar ta wallafa a shafin X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Igweh ya ba da umarnin fara bincike domin tabbatar da an zakulo wadanda suka yi ajalin Janar din a Abuja.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, SP Adeh Josephine ta tabbatar a yau Lahadi 23 ga watan Yunin 2024.

Wane mataki ƴan sanda suka ɗauka?

Josephine ta ce kwamishinan ya kaɗu da lamarin tare da tura sakon ta'azzara ga iyalan marigayin inda ya yi alkawarin tabbatar da adalci a binciken.

"Dadi da kari kwamishinan ya tabbatar da himmatuwar rundunar wurin dakile matsalolin tsaro a birnin Abuja wurin amfani da dabaru daban-daban."

- Adeh Josephine

Josephine ta tabbatarwa da al'umma ci gaba da ba da sanarwa duk lokacin da aka samu karin bayani.

Kara karanta wannan

Ana tsaka da rikicin sarauta, ƴan bindiga sun kai hari Masallaci, sun sace basarake

Ƴan bindiga sun sace Fasto a Zamfara

A wani labarin, kun ji cewa wasu ƴan bindiga sun kutsa har cikin gida inda suka sace malamin coci a jihar Zamfara.

Maharan sun sace Rabaran Mika Sulaiman a gidansa da ke birnin Gusau a jihar da ke Arewa maso Yamma a Najeriya.

Lamarin ya faru ne a ranar Asabar 22 ga watan Yunin shekarar 2024 da muke ciki kamar yadda rundunar yan sanda ta tabbatar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.