Zambar Naira Miliyan 22: EFCC Ta Cafke Ma’aikacin Karya a Fadar Shugaban Kasa

Zambar Naira Miliyan 22: EFCC Ta Cafke Ma’aikacin Karya a Fadar Shugaban Kasa

  • Jami’an hukumar EFCC sun kama wata kungiyar ma’aikatan gidan gwamnatin tarayya na bogi bisa laifin damfarar mutane
  • EFCC ta ce ta kama wadanda ake zargin bayan sun karbi Naira miliyan 22 daga hannu jama'a da sunan za su ba su ayyukan yi
  • Wadanda ake zargin sun baiwa EFCC bayanai masu amfani kuma za a gurfanar da su gaban kotu bayan kammala bincike

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Hukumar EFCC ta ce jami’anta sun kama wani ma'aikacin fadar shugaban kasa na jabu da wasu mutum 4 bisa zargin badakalar ba da ayyukan yi a Abuja.

A ranar Juma’a ne kakakin EFCC, Dele Oyewale, ya ce an kama wadanda ake zargin ne da laifin hada baki, wakilci na karya da kuma karyar samawa mutane aiki.

Kara karanta wannan

Rigima ta kaure tsakanin ‘yan bindiga, su na ta kashe junansu da kansu a jejin Zamfara

EFCC ta kama ma'aikatan gwamnatin tarayya na jabu
EFCC ta kama ma'aikacin fadar shugaban kasa na jabu bisa zargin zambar N22m. Hoto: @officialEFCC
Asali: Facebook

Damfara: EFCC ta kama ma'aikata na jabu

Sanarwar da aka wallafa a shafin EFCC na intanet ta bayyana sunayen masu laifin da: Augustine Enamegbai Umogboi, Eleojo Josephine Idakwo, Kingsley Onuh.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sauran sun hada da Omata Sunday da kamfanin Eljayon Nigeria Limited, wanda suke amfani da asusun bankinsa wajen karbar kudi daga hannun wadanda suka zambata.

Mutanen sun yi ikirarin baiwa wadanda suka damfara aiki a ma’aikatar sadarwa, kamfanin NNPC, hukumar FRSC da sauran ma’aikatun tarayya.

Yayin da Umogboi ya yi ikirarin cewa shi tsohon ma'aikacin Aso Rock ne, Idakwo ya yi ikirarin cewa shi ma’aikacin ma’aikatar yada labarai na bogi ne; Onoh kuma ya yi ikirarin ya kammala bautar kasa (NYSC).

"Ma'aikatan jabu sun yi zambar N22m" - EFCC

Sanarwar ta zargi wadanda aka kama da mallakar asusun bankuna daban-daban inda suke karbar kudaden da suka kai Naira miliyan 22,350,000 daga hannun mutane daban-daban.

Kara karanta wannan

EFCC ta gurfanar da ma'aikacin gwamnati gaban Kotu saboda zargin hana bincike

Da dama daga cikin wadanda abin ya shafa sun bayyana bakin cikin su a jerin korafe-korafen da suka rubuta wa hukumar ta EFCC, in ji rahoton Channels TV.

Wadanda ake zargin sun baiwa EFCC bayanai masu amfani kuma hukumar ta ce za ta gurfanar da su gaban kotu bayan kammala bincike.

An kashe mai tallata addini a Bauchi

A wani labarin, mun ruwaito cewa wasu fusatattun matasa a kauyen Nasaru da ke jihar Bauchi sun halaka wani matashi mai tallata wani sabon addini a yankin.

Majiyoyi na zargin cewa wasu matasa ne suka yi wa Yunusa Usman dukan tsiya har ya mutu saboda kalaman batanci ga Annabi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.