Yadda Kwankwaɗar Kunun Aya Ya Hallaka Mutane 24, Gwamna Ya Dauki Mataki Mai Tsauri
- Akalla mutane 24 ne suka mutu a jihar Lagos saboda zargin shan kunun aya wanda ba a masa rijista ba
- Gwamnatin jihar ta tabbatar da rasa rayuka tare da cewa mutane 34 sun kamu da cutar kwalara dalilin shan kunun aya
- Hadimin gwamnan jihar a bangaren lafiya, Kemi Ogunyemi shi ya tabbatar da haka inda ya ce ana ci gaba da bincike
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Lagos - Gwamnatin jihar Lagos ta yi martani bayan mutane 24 sun mutu saboda cutar kwalara.
A jiya Juma'a 21 ga watan Yunin 2024 an samu rasa rayukan mutane 24 da ƙaruwar kamuwa da cutar ga mutane 34.
Lagos: Gwamnati ta magantu kan cutar kwalara
Hadimin Gwamna Babajide Sanwo-Olu, Kemi Ogunyemi shi ya bayyana haka yayin hira da jaridar Punch a yau Asabar 22 ga watan Yunin 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ana zargin wadanda suka kamu da cutar sun sha kunun aya ne wanda yake da matsala a karamar hukumar Eti-Osa a jihar.
Gwamnati ya ce ta ziyarci asibitin inda mafi yawan marasa lafiyar suka tabbatar da shan kunun ayan ne sanadi.
Gwamnatin Lagos ta dauki muhimmin mataki
Daga bisani gwamnatin ta dauki samfuri na kunun ayan domin gwajin cutar kwalara.
"Mun samu robobin kunun ayan dauke da suna amma babu rijista daga hukumar NAFDAC da ke da alhakin kula da su."
"Mun samu lambobin waya a jikin kwalaben mun kira domin tsananta bincike amma ba su shiga."
"Mafi yawan kwalaben babu komai a ciki bare mu taba mu ji ko cutar tana ciki amma muna ci gaba da bincike."
- Kemi Ogunyemi
Hajjj: Jigon APC daga legas ta rasu
A wani Labarin, kun ji cewa Hukumomi sun sanar da rasuwar wata Hajiya daga jihar Lagos kuma jigon jam'iyyar APC a kasar Saudiyya.
Marigayiyar mai suna Ramota Bankole ƴar asalin jihar Lagos ta rasu a kasar yayin da ta ke aikin hajjin wannan shekara ta 2024.
Bankole kafin rasuwarta, ita ce tsohuwar sakatariyar jin dadi ta jam'iyyar APC a jihar Lagos wacce ta rike mukamin na tsawon lokaci.
Asali: Legit.ng