Dakarun Sojoji Sun Ceto Mata da Yaran da 'Yan Ta'adda Suka Sace

Dakarun Sojoji Sun Ceto Mata da Yaran da 'Yan Ta'adda Suka Sace

  • Rundunar sojojin Najeriya ta sanar da cewa dakarunta sun samu nasarar ceto wasu mutane da ƴan ta'adda suka sace a jihar Borno
  • Dakarun sojojin sun ceto mata bakwai da mata tara bayan sun farmaki maɓoyar ƴan ta'adda a ƙaramar hukumar Gwoza ta jihar
  • Jami'an tsaron tare da haɗin gwiwar ƴan banga sun kuma ɗan ta'adda ɗaya tare da kwato makamai masu yawa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Borno - Dakarun sojojin Najeriya a jihar Borno sun ceto mata bakwai da yara tara da ƴan ta'adda suka sace daga gidajensu.

An kuɓutar da mutanen ne a wasu jerin ayyukan yaƙi da ta’addanci da sojoji tare da haɗin gwiwar ƴan banga suka gudanar.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun kashe ƴan bindiga 220, sun ƙwamuso wasu sama da 300 a Najeriya

Sojoji sun kubutar da mutane daga wajen 'yan ta'adda a Borno
Sojoji sun ceto mata da yara daga hannun 'yan ta'adda a Borno Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Facebook

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da rundunar sojojin ta sanya a shafinta na X a ranar Juma'a, 21 ga watan Yunin 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda sojoji suka ceto mutanen da aka sace

Sanarwar ta kuma ƙara da cewa an hallaka ɗan ta'adda mutum ɗaya tare da ƙwato makamai a yayin samamen.

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

"A ƙaramar hukumar Gwoza da ke jihar Borno, sojoji sun aiwatar da wani harin kwantan ɓauna da aka kai a wuraren da ƴan ta’adda ke zaune a Pulka da Ashagashiya."
"A yayin samamen, sojojin sun yi musayar wuta da ƴan ta’addan, inda suka kashe mutum ɗaya, yayin da wasu suka gudu cikin ruɗani, suka bar kayayyakinsu."
"Sojojin sun yi nasarar kubutar da mata bakwai da kananan yara tara daga hannun ƴan ta’addan."
"Sojojin sun kuma samu nasarar kwato bindiga guda ɗaya, babura guda uku, barguna guda huɗu, kayayyakin girki, da sauran kayayyaki da dama."

Kara karanta wannan

Murna ta koma ciki, 'yan bindiga sun hallaka Amarya mako 1 tak bayan ɗaura aurenta

Har ila yau, rundunar sojin ta ce sojoji sun yiwa ƴan ta’adda kwanton bauna a yankin Komala da ke jihar Borno, inda suka kashe ɗan ta’adda guda ɗaya tare da ƙwato makamai.

Sojoji sun cafke masu garkuwa da mutane

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun bataliya ta shida ta sojojin Najeriya sun kama wasu riƙaƙƙun masu garkuwa da mutane biyu da suka addabi jihar Taraba.

An samu nasarar cafke waɗanda ake zargin ne, Fankau Algaji Laulo da Ahmadu Buba Ango a wani samamen rundunar hadin gwiwa ta sojoji da mafarauta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng