Zamfara: Ana Kukan Babu Kudi, Gwamnati Ta Fara Aikin Filin Jirgin Saman N62bn

Zamfara: Ana Kukan Babu Kudi, Gwamnati Ta Fara Aikin Filin Jirgin Saman N62bn

  • Gwamnatin tarayya ta kaddamar da aikin gina jirgin saman kasa da kasa a jihar Zamfara wanda ake sa ran kammala shi cikin watanni 30 masu zuwa
  • Ministan harkokin jirage, Festus Keyamo ne ya kaddamar da aikin da aka shirya kashe N62.8bn, inda ya ce ana barin jihar Zamfara a baya a bangaren nan
  • Gwamnan jihar, Dauda Lawal Dare wanda ya yi farin ciki da aikin ya yi fatan zai daukaka Zamfara a idon duniya ta fuskar kasuwanci, noma da yawon bude idanu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Zamfara- Ministan harkokin sufurin jirgin sama, Festus Keyamo ya dora harsashin fara aikin katafaren jirgin sama a Zamfara da rashin tsaro ya dabaibaye a wani yunkuri da bunkasa jihar.

Kara karanta wannan

EFCC ta gurfanar da ma'aikacin gwamnati gaban Kotu saboda zargin hana bincike

Filin jirgin na kasa da kasa da za a gina a Gusau zai lashe N62.8bn, kuma ana sa ran zai bunkasa tattalin arziki musamman a bangarorin noma, ilimi da yawon bude idanu.

Zamfara
An kaddamar da aikin filin jirgi kan N62.8bn a Zamfara Hoto: Dauda Lawal
Asali: Facebook

A sakon da Gwamna Dauda Lawal Dare ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya ce idan filin jirgin ya kammala, jihar Zamfara za ta kara daukaka a idon duniya ta fuskar kasuwanci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“An bar Zamfara a baya,” Ministan jirage

Festus Keyamo ya bayyana aikin katafaren filin jirgin sama da aka kaddamar a jihar Zamfara da cewa zai cicciba jihar ta bangarori da dama.

Vanguard News ta wallafa Ministan na cewa ;

“ Ina fadin cewa a yankin Arewa maso Yamma, jihar Zamfara ba ta samun irin wadannan manyan ayyukan ci gaba.
Sauran sassan na da filayen jirgin sama masu kyau, mutanen da ke zaune a yankin na iya amfani da su, amma ita Zamfara an bar ta a baya.”

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun mamaye dajin Kainji, gwamnatin tarayya ta dauki mataki

A jawabinsa, gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal Dare ya yi alkawarin za a kammala aikin jirgin saman cikin watanni 30.

Gwamna Dauda ya karrama askarawan Zamfara

A baya mun kawo labarin cewa gwamnan Zamfara, Dauda Lawal Dare ya karrama askawaran jihar da suke kokarin kawar da rashin tsaro a sassan jihar

Askarawa 20 gwamnan ya karrama da ya ce suna taka rawa wajen dakile ta'addancin da ya addabi sassan Zamfara, sannan ya yi alkawarin taimakawa iyalan wadanda suka rasu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.