Hukuncin Masarautar Kano ya Lasawa Bangarorin Da Ke Rikici Zuma a Baki
- A yammacin Alhamis aka sa rai dambarwar masarautar Kano za ta zo karshe a zaman kotun da ya yanke hukunci kan rikicin waye halastaccen sarkin Kano biyo bayan rushe masarautu
- Amma hukuncin ya jefa al’umma cikin rudani yayin da aka lasawa bangarorin biyu zuma na cewa su ne da nasara bayan kotun ta jingine dokar da ta maido Muhammadu Sanusi II
- Amma gwamnatin Kano ta kafe kan cewa hukuncin bai taba muhibbar dokar da ta rushe masarautu ba, saboda haka dole ne Sarki na 15 Aminu Bayero ya fice daga fadar Nassarawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano- Hukuncin da babbar kotun tarayya ta yanke kan batun rikicin masarautar Kano ya bar baya da kura, inda bangarorin biyu da ke cikin dambarwar ke ganin su ne da nasara.
A shari’ar da ya yanke ranar Alhamis, Mai shari’a Abdullahi Muhammad Ladan ya jingine dokar da aka yi amfani da ita wurin maido da Malam Muhammadu Sanusi II karagarsa.
Daily Trust ta wallafa cewa Mai shari’a Muhammad Ladan ya ce hukuncin bai soke dokar da rushe masarautun Kano da majalisar dokokin jihar ta samar ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnati ta hakikance kan tsige Aminu Bayero
Gwamnatin jihar Kano ta hakikance kan cewa hukuncin da kotu ta yanke a yammacin Alhamis ya tabbatar da tsige sarkin Kano 15, Aminu Ado Bayero yayin da ta umarci a fitar da shi daga fadar sarki ta Nassarawa.
A sanarwar da darakta janar na gwamna kan yada labarai, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya wallafa a shafinsa na facebook, babu inda hukuncin ya soke dokar da ta tumbuke rawanin Sarki Bayero.
Aminu Dan’agundi ya ce sun yi nasara
A rahoton da Leadership News ta wallafa, tsagin Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero ya shiga murnar samun nasara a kotun tarayya, haka ma gwamnatin Kano.
Tun da fari, Sarkin Dawaki babba, Aminu Babba Dan’agundi ta bakin lauyansa, Idris Aliyu Nassarawa ya nemi kotu ta rushe dokar da ta tsige masarautun Kano.
Rikicin masarauta: Kotu ta yanke hukunci
A baya mun kawo labarin cewa babbar kotun tarayya da ke zamanta a kano karkashin mai shari’a Abdullahi Muhammad Liman ta yanke hukunci kan dambarwar masarauta.
Mai shari’a na ganin gwamnati ta yi biris da umarninsa na farko, wanda ya sa ya jinge dokar da ta maido da Sanusi II karagarsa, amma ta ce hakan bai soke dokar da ta rushe masarautu ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng