Ana Cikin Rigimar Sarautar Kano, Miyagu Sun Yi Ta'asa Har da Jikkata Ƴan Sanda

Ana Cikin Rigimar Sarautar Kano, Miyagu Sun Yi Ta'asa Har da Jikkata Ƴan Sanda

  • Yayin da ake tsaka da shari'ar sarautar Kano, wasu miyagu sun hallaka mutum daya da jikkata jami'an ƴan sanda
  • Miyagun sun yi ajalin mutumin mai suna Muktar Garba da aka fi sani da Babalia a yankin Jaen Makera da ke Kano
  • Wannan na zuwa ne yayin da aka dage ci gaba da sauraran shari'ar da zuwa karfe biyu na ranar yau Alhamis

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Wasu miyagu a jihar Kano sun kai farmaki inda suka hallaka mutum daya da jikkata ƴan sanda biyu.

Lamarin ya faru ne a unguwar Jaen Makera da ke birnin Kano ana tsaka da shari'ar sarautar jihar.

Kara karanta wannan

Najeriya ta yi rashi, fitaccen Sarki mai daraja ya riga mu gidan gaskiya a Landan

An hallaka wani da jikkata ƴan sanda 2 a Kano
An rasa rai a Kano yayin da aka jikkata jami'an 'yan sanda 2. Hoto: Nigeria Police Force.
Asali: Facebook

Kano: Miyagu sun hallaka wani matashi

Kwamishinan ƴan sanda, Hussaini Gumel ya tabbatar da haka a yau Alhamis 20 ga watan Yunin 2024 a Kano a cewar Premium Times.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gumel ya ce miyagun sun yi ajalin wani mai suna Muktar Garba da aka sani da Babaliya yayin ta'asar, Daily Nigerian ta tattaro.

Kwamishinan ya ce Muktar ya rasu ne a asibitin kwararru na Murtala Mohammed da ke Kano.

Har ila yau, ya ce an mika gawar marigayin ga yan uwansa domin binne shi kamar yadda tsarin Musulunci ya koyar.

An dage sauraran shari'ar sarauta a Kano

Wanann na zuwa ne yayin da ake tsaka da shari'ar sarautar jihar a yau Alhamis 20 ga watan Yunin 2024.

Kotun ta dage zaman zuwa karfe biyu na ranar yau Alhamis domin ci gaba da sauraran shari'a kan halataccen Sarkin Kano.

Kara karanta wannan

Hajj 2024: Alhazai 600 ƴan ƙasa 1 sun mutu a Saudiyya, an gano silar ajalinsu

Ƴan sanda sun magantu kan shari'ar Kano

Kun ji cewa rundunar ƴan sanda reshen jihar Kano ta roƙi jama'a su zauna lafiya a lokacin da ake dakon hukuncin Babban Kotun Tarayya kan rigimar sarauta.

Hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da jami'in hulda da jama'a na rundunar ƴan sandan Kano, SP Abdullahi Kiyawa ya fitar a Kano ranar Alhamis.

Kiyawa ya kara nanata aniyar rundunar wurin tabbatar da kare rayukan mutane da kuma dukiyoyinsu a jihar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel