Sojoji Sun Kama Ɗan Ta’adda Yana Kokarin Guduwa Bayan Ya Kashe Mutane

Sojoji Sun Kama Ɗan Ta’adda Yana Kokarin Guduwa Bayan Ya Kashe Mutane

  • Rundunar sojin Najeriya ta kama ƙasurgumin ɗan ta'adda da ake zargi ya fitini ƙauyuka da dama a jihar Taraba da ke Arewa maso gabas
  • Rahoto ya nuna rundunar ta sanar da cewa ta bi sawun ɗan ta'addar ne bayan ya aikata ta'asa a wani kauye yana ƙoƙarin neman mafaka
  • Kwandan rundunar da ta kama ɗan ta'addar, Birgediya Janar Kingsley Chidiebere Uwa ya bayyana halin da ɗan ta'addar yake ciki

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Taraba - Rundunar sojin Najeriya ta sanar da kama dan ta'addar da ya fitini yankuna da dama a jihar Taraba.

Rundunar ta ce ta kama dan ta'addar mai Suna Ibrahim Hassan ne yayin da yake kokarin tserewa bayan sun kai hari kan wasu mutane.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun yi magana yayin da kotu ke shirin sanar da halataccen Sarkin Kano

Dan bindiga
Sojoji sun kama babban dan bindiga a Taraba. Hoto: HQ Nigerian Army
Asali: UGC

Legit ta tabbatar da haka ne a cikin sakon da rundunar sojin Najeriya ta wallafa a shafinta na Facebook a yau Alhamis.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An kai hari Mararaban Agazawa

Rundunar sojin Najeriya ta ce ɗan ta'addar mai suna Ibrahim Hassan ya kai mummunan hari garin Mararaban Agazawa da ke jihar Taraba.

Rahotanni sun nuna cewa harin ya jawo asarar rayuka biyar tare da jikkata mutane da dama da satar dukiya.

An kama wanda ya kai hari Mararaba

Rundunar sojin ta ce biyo bayan harin, cikin gaggawa ta tsunduma neman 'yan ta'addar a ranar 16 da watan Yuni.

Ana cikin haka ne rundunar ta cafke shugaban ƴan ta'addar da suka kai harin kuma ta kwato makamai a wajensa da babur da suka sace yayin harin.

Dan ta'addan da ake zargi ya amsa laifi

Shugaban rundunar, Birgediya Janar Kingsley Chidiebere Uwa ya ce ɗan ta'addar ya amsa laifin kai harin garin Mararaban Agazawa da sauran wurare a jihar Taraba.

Kara karanta wannan

Murna ta koma ciki, 'yan bindiga sun hallaka Amarya mako 1 tak bayan ɗaura aurenta

Birgediya Janar Kingsley Chidiebere Uwa ya kuma tabbatar da cewa a yanzu haka ana cigaba da bincike domin daukan mataki na gaba kan ɗan ta'addar

Gwamna ya yi kira ga jami'an tsaro

A wani rahoton, kun ji cewa gwamna Caleb Mutfwang na jihar Filato ya taya hafsoshin tsaron Najeriya da sufetan yan sanda na kasa murna.

Ya ce yana da yaƙinin cewa suna da gogewar da zasu iya magance matsalar tsaron da ta addabi jihar Filato da yankunan Najeriya baki ɗaya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Online view pixel