LABARI DA DUMI-DUMI: An kama wani Babban dan ta'adda

LABARI DA DUMI-DUMI: An kama wani Babban dan ta'adda

– Jami’an Hukumar DSS tayi wani babban kamu

– An damke daya daga cikin manyan ‘yan ta’addan duniya a Najeriya

– Yanzu haka Shugaba Barrack Obama ya kira Shugaba Muhammadu Buhari a waya

LABARI DA DUMI-DUMI: An kama wani Babban Dan Ta'adda
LABARI DA DUMI-DUMI: An kama wani Babban Dan Ta'adda

Hukumar DSS ta damke daya daga cikin manyan ‘yan ta’addan duniya a cikin kasar nan. Har yanzu dai ba a bayyana suna ba saboda ana cikin bincike. Wannan mutumi da aka kama shine na uku a jerin ‘Yan ta’ddan Duniya gaba daya.

Kwanakin nan ne kuma Hukumar ta liken asiri ta gano wani yunkuri na kai hari a Kasar Amurka. Jaridar The Nation ce dai ta bayyana wannan labari; tace an kama Babban Dan ta’addan Duniya a cikin Kasar nan.

KU KARANTA: Shugaba Buhari zai sauya Ministoci

Ana zargin wannan Dan ta’adda da kashe mutane a Duniya daga shekarar 2012 zuwa ta 2013. Yanzu haka dai Jami’an tsaro daga ko ina a Duniya sai barkowa suke yi cikin Kasar domin su gana da wannan Dan ta’adda suyi masa tambayoyi.

Ba a dai ba da sun aba har yanzu saboda halin bincike. Tuni dai har Shugaban Kasar Amurka ya kira Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya domin jin yadda abin ya faru.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita @naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel