Najeriya Ta Yi Rashi, Fitaccen Sarki Mai Daraja Ya Riga Mu Gidan Gaskiya a Landan

Najeriya Ta Yi Rashi, Fitaccen Sarki Mai Daraja Ya Riga Mu Gidan Gaskiya a Landan

  • Fitaccen basarake a jihar Ogun, Oba Olufemi Ogunleye ya mutu a wani asibiti a Landan ranar Laraba, 19 ga watan Yuni, 2024
  • Rahotanni sun nuna cewa Sarkin ya rasu ne bayan fama da gajeruwar rashin lafiya yana da shekara 79 a duniya
  • Marigayi ya kasance tsohon ɗan jarida wanda ya yi aiki da tsohuwar jaridar Daily Times kuma ya yi ritaya daga aikin gwamnati

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Ogun - Sarkin Akinale wanda ake kira da Towulade na Akinale a ƙaramar hukumar Ewekoro da ke jihar Ogun, Oba Olufemi Ogunleye ya riga mu gidan gaskiya.

Fitaccen basaraken mai daraja ya rasu ne yana da shekaru 79 a duniya ranar Laraba, 19 ga watan Yuni, 2024.

Kara karanta wannan

Matasan Bauchi sun yi ajalin Yunusa kan zargin furta kalaman batanci ga Annabi SAW

Oba Olufemi Ogunleye
Allah ya yi wa wani sarki a jihar Ogun, Oba Olufemi Ogunleye rasuwa Hoto: Aba Hafa
Asali: Facebook

Jaridar Vanguard ta tattaro cewa Sarkin ya sha fama da rashin lafiya a wasu lokuta daban-daban kuma ana kai shi asibitin St. Thomas da ke Landan a ƙasar Ingila.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yaushe Sarkin ya mutu?

Sai dai a wannan karon Allah ya karɓi rayuwarsa da yammacin ranar Laraba a asibitin Landan, Punch ta ruwaito hakan.

Wata majiya da ke da kusanci da marigayi Sarkin, ta shaida wa manema labarai cewa marigayin bai jima da kammala karatun digiri na uku a fannin shari’a ba.

"Towulade na Akinale, Oba Olufemi Adewunmi Ogunleye ya riga mu gidan gaskiya yana da shekaru 79 a duniya a wani asibitin Landan bayan gajeruwar rashin lafiya."
"Muna addu'ar ruhinsa ya samu salama a wurin Ubangiji, Amin."

Takaitaccen tarihin Sarki Ogunleye

Marigayi Oba Ogunleye ya kasance babban dan jarida wanda ya yi aiki da tsohuwar fitacciyar jaridar nan Daily Times ta Najeriya.

Kara karanta wannan

Ana cikin rigimar sarautar Kano, miyagu sun yi ta'asa har da jikkata yan sanda

Ya yi ritaya daga aiko a lokacin yana matsayin manajan sashen hulda da jama'a na kamfanin sufurin jiragen sama na Najeriya watau Nigeria Airways da aka rushe.

Tsohon Gwamna Gbenga Daniel ne ya fara nada shi a matsayin Baale na Akinale a shekarar 2004 kuma yana cikin wadanda wannan gwamnatin ta ɗaga darajarsu zuwa Oba a 2006.

Alhazan Masar 60 sun rasu a Saudiyya

A wani rahoton kuma ƴan uwa da abokan arziki na ci gaba da laluben Alhazan ƙasar Masar da suka ɓace ranar Laraba, 19 ga watan Yuni, 2024.

Bayanai sun nuna cewa akalla alhazai 600 da suka fito daga Masar ne suka riga mu gidan gaskiya a ƙasa mai tsarki a lokacin aikin Hajjin bana.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262