"Umarnin Tinubu Na Ke Jira": Gwamna Idris Ya Bayyana Matsayarsa Kan Mafi Karancin Albashi

"Umarnin Tinubu Na Ke Jira": Gwamna Idris Ya Bayyana Matsayarsa Kan Mafi Karancin Albashi

  • Yayin da ake tababa da gwamnoni kan mafi karancin albashi, Gwamna Nasir Idris na Kebbi ya bayyana matsayarsa
  • Kwamred Idris ya ce a shirye yake domin biyan mafi karancin albashi da duk aka amince da shi komai yawansa kuwa
  • Gwamnan ya ce zai ci gaba da ba ma'aikata kulawa na musamman domin ci gabansu da kuma walwala a halin da ake ciki

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kebbi - Gwamna Nasir Idris na jihar Kebbi ya bayyana matsayarsa kan biyan mafi karancin albashi.

Kwamred Idris ya barranta kansa da sauran gwamanonin jihohi kan matsayarsu game da karin albashi.

Gwamna Idris ya bayyana matsayarsa kan mafi karancin albashi
Gwaman Nasir idris ya bayyana matsayarsa kan biyan mafi karancin albashi a Kebbi. Hoto: Kebbi Satate Government, Nigeria Labour Congress HQ.
Asali: Facebook

Gwamna ya shirya biyan mafi karancin albashi

Kara karanta wannan

"Ya kamata gwamnati ta gyara albashi, farashi na kara hauhawa," Tsohon ministan Buhari

Gwamnan ya bayyana haka ne a yau Laraba 19 ga watan Yuni inda ya ce ba shi da masaniya kan matakin gwamnonin a cewar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce zai biya ma'aikata duk abin da Bola Tinubu ya yanke hukunci game da mafi karancin albashi.

"Ba na cikin ganawar da aka yi, ko da ina ciki ba kasance cikin wadanda ba za su iya biya ba."
"Kamar yadda na ke fada, na shirya biyan mafi karancin albashi da aka amince da shi, ina kan baka na."

- Gwana Nasir Idris

Gwamna Idris zai ba ma'akatan Kebbi kulawa

Gwamnan ya kuma bayyana himmatuwarsa wurin ba ma'aikata kulawa na musamman duba da halin da ake ciki.

Ya ce a matsayinsa na mamban kwamitin mafi karancin albashi zai ci gaba ba ma'aikata goyon baya musamman abin da ya shafi walwalarsu.

Kara karanta wannan

Sabon albashi: Ɗan PDP ya ba Tinubu shawarar abin da ya kamata ya biya ma'aikata

Hakan ya biyo bayan fatali da mafi karancin albashin N62,000 da gwamnoni suka yi inda suka ce ba za su iya biya ba.

Ma'aikata sun tura sako ga gwamnoni

A wani labarin, kun ji cewa wasu ma'aikata a Najeriya sun bukaci gwamnonin jihohi su biya su hakkokinsu.

Ma'aikatan sun bukaci gwamnonin su rage albashinsu da alawus domin biyan mafi karancin albashi a jihohi.

Wannan na zuwa ne bayan kungiyar gwamnonin ta bayyana cewa ba za ta iya biyan mafi karancin albashi na N62,000 ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel