Jami'ar Kaduna ta koma karatu, ta bukaci iyaye su sa hannu kan wasu takardun alkawari

Jami'ar Kaduna ta koma karatu, ta bukaci iyaye su sa hannu kan wasu takardun alkawari

  • Jami'ar jihar Kaduna ta bada umarni ga malamai da dalibai da su koma karatu a ranar Talata
  • Rijistran makarantar, Samuel Manshop, ya sanar da cewa dole iyayen dalibai su saka hannu kan wata takardar alkawari
  • Alkawarin da zasu dauka kuwa shine 'ya'yansu zasu kasance masu dabi'a tagari idan sun dawo makaranta

Jami'ar jihar Kaduna ta bada umarni ga tsoffin dalibai da kuma sabbi da su dawo karatun shekarar 2020/2021 a ranar 22 ga watan Yuni.

Makarantar ta ce dole ne iyayen sabbi da tsoffin dalibai su saka hannu kan wata takardar alkawari cewa 'ya'yansu zasu kasance nagari.

Rijistran makarantar, Samuel Manshop, ya bada wannan umarnin a wata takardar da ya fitar a ranar Talata a Kaduna, Daily Nigerian ta ruwaito.

KU KARANTA: Imanin da nayi da matasan Najeriya har yanzu yana nan daram, Aisha Buhari

Jami'ar Kaduna ta koma karatu, ta bukaci iyaye su sa hannun kan wasu takardun alkawari
Jami'ar Kaduna ta koma karatu, ta bukaci iyaye su sa hannun kan wasu takardun alkawari. Hoto daga dailynigerian.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Lawan: Bayan saukar mulkin Buhari, akwai yuwuwar APC ta fuskanci kalubale

"Hukumar jami'ar jihar Kaduna tana sanar da malamai, dalibai da sauran jama'a cewa zata fara karatun shekarar 2020/2021 kuma zata fara a ranar talata.

"Bugu da kari, ana tsammanin iyaye da masu daukar nauyin sabbi da tsoffin dalibai su saka hannu kan takardar alkawari a sashen karatun 'ya'yansu.

“Takardar zata tabbatar da cewa 'ya'yansu zasu kasance masu dabi'a tagari," takardar tayi bayani.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya ruwaito cewa jami'ar ta dakatar da karatu a ranar 8 ga watan Yuni har sai baba ta gani.

Rijistran makarantar wanda bai bada dalilin dakatar da karatun ba, yace dalibai masu digiri kadai ya shafa banda masu karatun digiri na biyu da na uku, lafiya, hada magunguna, The Nation ta ruwaito.

A wani labari na daban, mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbaji ya ce yana da tabbacin cewa Najeriya zata cigaba da zama kai hade a matsayin kasa daya duk da masu son ganin rabuwarta.

Ya sanar da haka a ranar Litinin a Abuja yayin taron farko na matasan jam'iyyar APC, Channels TV ta ruwaito.

"A bangaren son kawo hargitsi da rabewar kai, zan iya cewa mun fi karfi idan muna tare kuma a ganin duk masu fatan ganin rabewar kasar nan, basu kyauta ba," Farfesa Osinbajo ya sanar da taron matasa da masu ruwa da tsaki na APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng