Ana Tsaka da Ricikin Siyasa: Gwamnan PDP Ya Rantsar da Sababbin Ciyamomi 23 a Jiharsa
- Gwamna Siminialayi Fubara na Ribas, ya rantsar da sababbin shugabannin kwamitocin riko na kananan hukumomi 23 na jihar
- An gudanar da bikin rantsuwar ne a gidan gwamnatin jihar dake Fatakwal, babban birnin jihar a safiyar Laraba
- Wannan na zuwa ne bayan da gwamnan ya aike da sunayen shugabannin rikon zuwa majalisar jihar domin tantance su
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Fatakwal, Jihar Ribas - Gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara, ya rantsar da sababbin shugabannin riko na kananan hukumomi 23 na jihar.
An yi bikin rantsuwar ne a ranar Laraba a gidan gwamnati da ke Fatakwal, babban birnin jihar cikin tsauraran matakan tsaro.
Majalisar Ribas ta tantance ciyamomi 23
Gidan talabijin na Channels ya rawaito cewa an gudanar da bikin ne a zauren majalisar zartarwar jihar inda kashin farko na shugabannin rikon su 11 suka karbi rantsuwa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hakan na zuwa ne kwana guda bayan Fubara ya mika jerin sunayen ga majalisar dokokin jihar karkashin jagorancin kakakin majalisar, Victor Jumbo.
‘Yan majalisar dai sun gayyaci wadanda aka mika sunayensu domin tantance su da misalin karfe 8:00 na safiyar Laraba, inji rahoton Vanguard.
Jerin sunayen ciyamomin da aka rantsar
Duba sunayen shugabannin riko 23 da Fubara ya rantsar da su a kasa:
Sunan ciyaman | Karamar hukuma | |
1 | Madigai Dickson | Abua/Odua |
2 | Happy Benneth | Ahoada ta Gabas |
3 | Mr. Daddy John Green | Ahoada ta Yamma |
4 | Otonye Briggs | Akuku Toru |
5 | Reginald Ekaan | Andoni |
6 | Orolosoma Amachree | Asari Toru |
7 | Alabota Anengi Barasua | Bonny |
8 | Anthony Soberekon | Degema |
9 | Brain Gokpa | Eleme |
10 | David Omereji | Emouha |
11 | John Otamiri | Etche |
12 | Kenneth Kpeden | Gokana |
13 | Darlington Orji | Ikwerre |
14 | Marvin Yobana | Khana |
15 | Chijioke Ihunwo | Obia/Akpor |
16 | Princewill Ejekwe | Ogba/Egbema/Ndoni |
17 | Evans Bipi | Ogu/Bolo |
18 | Princess Ogan | Okrika |
19 | Promise Reginald | Omuma |
20 | Enyiada Cookey-Gam | Opobo/Nkoro |
21 | Gogo Philip | Oyigbo |
22 | Ichemati Ezebunwo | Port Harcourt |
23 | Matthew Dike | Tai |
Obasanjo ya magantu kan nasarar gwamnatinsa
A wani labarin, mun ruwaito Olusegun Obasanjo ya bugi kirji da cewa gwamnatinsa na daga cikin mafi nagarta wajen gudanar da mulki a tarihin Najeriya.
Olusegun Obasanjo ya ce gwamnatinsa na daga cikin mafi nagarta wajen gudanar da mulki a tarihi, wanda ta taimakawa dimokuraɗiyyar kasar na shekaru 25.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng