Rigimar Sarautar Kano Ta Ƙara Tsananta, Majalisa Ta Garzaya Kotun Ɗaukaka Ƙara

Rigimar Sarautar Kano Ta Ƙara Tsananta, Majalisa Ta Garzaya Kotun Ɗaukaka Ƙara

  • Yayin da taƙaddama kan sarautar Kano ke ƙara ƙamari, majalisar dokokin jihar ta shigar ƙara a gaban kotun ɗaukaka ƙara
  • Majalisar ta buƙaci kotun ɗaukaka kara ta dakatar da shari'ar sarauta da ke gaban babbar kotun tarayya, kana ta dawo da ita gabanta
  • Tuni dai Babban Kotun Tarayya mai zama a Kano ta shirya yanke hukunci kan halascin tube Sarki na 15, Aminu Ado Bayero da sarakuna hudu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kano - Majalisar dokokin jihar Kano ta garzaya kotun ɗaukaka ƙara kan rigimar sarautar da ta ƙi ci kuma ta ƙi cinyewa a jihar.

Majalisar ta roƙi kotun ɗaukaka ƙara ta dakatar da shari'ar da Sarkin Dawaki Babba, Aminu Babba Danagundi ya shigar gaban babban kotun tarayya.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Abba ta bayyana matsayarta kan tarar N10 da aka sanya mata kan Aminu Ado

Sarki Sanusi II da Aminu Ado.
Majalisar dokokin jihar Kano ta ɗaukaka kara kan rigimar masarautar Kano Hoto: Sanusi Lamido Sanusi, Imran Muhammad
Asali: UGC

An kai karar masarautar Kano babban kotu

Kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito, Aminu Ɗanagundi ya ƙalubalanci sabuwar dokar masarautar Kano, 2024 wanda ta tube sarakuna biyar na jihar Kano.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai ƴan majalisar sun buƙaci kotun ɗaukaka ƙara ta dawo da shari'ar hannunta saboda yadda ake samun saɓanin umarni tsakanin babbar kotun jiha da ta tarayya.

Mai shari’a Mohammed Liman na babbar kotun tarayya da ke Kano ya yanke hukuncin cewa kotun tana da hurumin sauraron ƙorafin Sarki na 15, Aminu Ado.

Ya kuma sanya ranar 20 ga watan Yunin da muke ciki domin yanke hukunci kan halascin sabuwar dokar masarauta wadda ta tsige Aminu da sauran sarakuna huɗu.

Majalisar dokokin Kano ta ɗaukaka ƙara

Bisa rashin gamsuwa da matakin, majalisar dokokin Kano ta hannun lauyanta, Eyitayo Fatogun (SAN) ta shigar da ƙara mai lamba CA/KN/ /26/2024 a kotun ɗaukaka ƙara.

Kara karanta wannan

Aminu Vs Sanusi II: Kotu ta shirya raba gardama, za ta sanar da sahihin Sarkin Kano

Lauyan ya roƙi kotun ɗaukaka ƙara ta dakatar da Alhaji Ɗanagundi a yunƙurinsa na soke sabuwar dokar masarautar Kano da dawo da tsohuwar dokar da majalisar ta warware, rahoton Guardian.

Ya buƙaci kotun ɗaukaka ƙarar ta dakatar da shari'ar da ke gaban babbar kotun tarayya na wucin gadi har sai ta yanke hukunci kan ƙarar da majalisa ta ɗaukaka.

Waɗanda ake tuhuma a ƙarar sun haɗa da Alhaji Ɗanagundi, gwamnatin Kano, Antoni Janar na Kano, sufetan ƴan sanda, kwamishinan ƴan sanda, hukumar NSCDC da DSS.

Kwankwaso ya fallasa maƙiyan Kano

A wani rahoton kun ji cewa jagoran NNPP na ƙasa ya bayyana yadda ƴan Kwankwasiyya suka sha fama da maƙiyan siyasa tun zaɓen 2019 har zuwa yau.

Rabiu Kwankwaso ya ce ga dukkan alamu waɗannan maƙiyan sun sake dawowa su wargaza Kano a rikicin sarautar da ke faruwa a halin yanzu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel