Sabon Albashi: Ɗan PDP Ya Ba Tinubu Shawarar Abin da Ya Kamata Ya Biya Ma’aikata

Sabon Albashi: Ɗan PDP Ya Ba Tinubu Shawarar Abin da Ya Kamata Ya Biya Ma’aikata

  • Dangane da sabon mafi karancin albashi, Reno Omokri ya dage cewa Najeriya ba za ta iya biyan adadin da 'yan kwadago ke nema ba
  • Omokri ya ce bai kamata gwamnatin Bola Tinubu ta aiwatar da mafi karancin albashin da gwamnatocin jihohi ba za su iya biya ba
  • Babban mai sharhi kan al'amuran zamantakewar al'umma ya bayyana cewa "sauki ko tsadar rayuwa ya bambanta a fadin Najeriya"

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Reno Omokri, wani mai sharhi kan al'amuran siyasa da zamantakewa ya ce Najeriya ba ta arzikin biyan abin da 'yan kwadago ke nema matsayin mafi karancin albashi ba.

Reno Omokri ya nemi gwamnatin Bola Tinubu da ta biya N75,000 matsayin mafi karancin albashi sannan ta baiwa jihohi damar biyan abin da za su iya, maimakon tilasta musu kan abin ba za su iya biya ba.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa ya bayyana hanyar da za a kawo ƙarshen tsadar rayuwa a Najeriya

Sabon mafi karancin albashi: Reno Omokri ya nemi Tinubu ya biya N75,000
Reno Omokri ya ba gwamnatin Tinubu shawara kan sabon mafi karancin albashi. Hoto: @NLCHeadquarters, @officialABAT
Asali: Facebook

Omokri ya kawo shawarar albashin N75,000

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na X a daren Laraba, dan jam'iyyar PDP mai zama a waje ya ce "biyan N75,000 da sakarwa jihohi mara zai nuna tsarin tarayya na gaskiya".

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Omokri ya wallafa cewa:

“Matsayata ita ce Najeriya ba ta da karfin arziki kuma ba za ta iya biyan duk wani adadi da kungiyar kwadago ta bukata ba kamar yadda Sule Lamido ya ambata.
“Ina ganin ya kamata gwamnatin tarayya ta biya N75,000 a matsayin sabon albashi, sannan ta bar jihohi su biya abin da za su iya, maimakon tilasta musu kan abin da ba za su iya ba."

Gwamna ya ƙara mafi ƙarancin albashi

A wani labarin makamancin wannan, mun ruwaito cewa gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki ya ƙarawa ma'aikatan jihar mafi ƙarancin albashi zuwa N70,000

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta yi biris da NLC, ta dage a kan biyan N62,000 ga ma'aikata

Gwamna Obaseki ya sanar da hakan ne a lokacin da ya je kaddamar da sabon ofishin 'yan kwadago na jihar, inda ya ce sabon albashin zai fara aiki 1 ga watan Mayun 2024.

Wannan na zuwa ne yayin da ƙungiyar kwadago ta ƙasa ke ta fafutukar ganin gwamnatin tarayya ta ƙara mafi ƙarancin albashi saboda tsadar rayuwa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel