El Rufai Ya Yi Magana Kan Binciken da Ake Yi Masa, Ya Fadi Makomar Uba Sani a Kaduna

El Rufai Ya Yi Magana Kan Binciken da Ake Yi Masa, Ya Fadi Makomar Uba Sani a Kaduna

  • Nasir El-Rufai, tsohon gwamnan jihar Kaduna, ya yi hasashen faɗuwar gwamnatin Gwamna Uba Sani wanda ya gaje shi
  • El-Rufai ya buƙaci magoya bayansa da su marawa gwamnatin Uba Sani baya da addu’a, kuma ka da su damu da matakin da aka ɗauka na bincike a kan gwamnatinsa
  • Tsohon gwamnan na jihar Kaduna ya bayyana cewa matakin da majalisar jihar ta ɗauka na bincikar gwamnatinsa bai dame shi ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmed El-Rufai, ya ce bai damu da yunƙurin da majalisar dokokin jihar ke yi na bincikar gwamnatinsa ba.

El-Rufai ya yi nuni da cewa mai yiwuwa gwamnatin ba za ta yi nasara ba.

Kara karanta wannan

Gwamna Fubara ya fallasa makarkashiyar da ake shiryawa kan magoya bayansa

El-Rufai ya magantu kan bincikensa a Kaduna
El Rufai ya yi hasashen makomar Uba Sani Hoto: @ubasanius, @elrufai
Asali: Twitter

Tsohon gwamnan na jihar Kaduna ya bayyana hakan a wani taron Sallah da ya yi da muƙarrabansa a ranar Talata 18 ga watan Yunin 2024, cewar rahoton jaridar Daily Nigerian.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me El-Rufai ya ce kan Uba Sani?

Kamar yadda jaridar Guardian ta ruwaito, El-Rufai ya kuma shawarce su da su guji yin cacar baki da hadiman gwamnan, inda ya yi hasashen cewa Uba Sani bayan ya gama ƴan tsalle-tsallensa, zai faɗo kamar alewa a hannun yaro.

"Ku tallafawa gwamna da ƴan majalisarsa da addu’o’i domin su yi abin da ya dace."
"Ka da ku ji zafi kan abin da ke faruwa. Idan ya gama ƴan tsalle-tsallen, zai faɗo kamar alewa (a hannun yaro)."

- Nasir Ahmad El-Rufai

El-Rufai da gwamnatin Uba Sani

Wannan dai shi ne karon farko da tsohon gwamnan ya yi magana a bainar jama'a tun bayan da rikici ya ɓarke tsakaninsa da magajinsa.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Abba ta bayyana matsayarta kan tarar N10 da aka sanya mata kan Aminu Ado

Duk da aminai ne, an ji yadda gwamnatin Uba Sani ta taso Nasir El-Rufai a gaba.

Tsohon jigo a APC ya caccaki Uba Sani

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon babban jigo a jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya, Salihu Muhammad Lukman ya yi kaca-kaca da gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, har ya ce ba zai zarce a ofis ba.

Tsohon mataimakin shugaban na jam’iyyar APC na ƙasa a yankin Arewa maso Yamma yana ganin Bola Tinubu da Malam Uba Sani ba za su yi nasarar komawa kujerunsu a shekarar 2027 ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng