Ana Cikin Talauci, Tinubu Ya Fadi Hanyar da Za Ta Zamo Mafita Ga ’Yan Najeriya

Ana Cikin Talauci, Tinubu Ya Fadi Hanyar da Za Ta Zamo Mafita Ga ’Yan Najeriya

  • Shugaban kasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya yi kira ga yan Najeriya kan abin da ya kamata su runguma domin yaki da fatara
  • Shugaban ya ce duk da cewa ana fama da talauci amma akwai abubuwan da idan ba a nisance su ba za su kara damuwa ga Najeriya
  • Bola Tinubu ya bayyana haka ne yayin da shugabannin majalisar tarayya suka kai masa ziyarar gaisuwar sallah a jihar Legas

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Lagos - Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya yi kira na musamman ga 'yan Najeriya kan canza hali.

Shugaban ya ce duk da cewa ana fama da talauci a kasar, yana da muhimmanci a fahimci cewa dabi'a nagari ne kawai mafita.

Kara karanta wannan

'Kar ka fara da bada hakuri': 'Yan kasa sun yi martani ga Tinubu, sun fadi mafita ga Najeriya

Shugaba tinubu
Bola Tinubu ya bukaci yan Najeriya su canza hali. Hoto: Aiswaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa shugaba Bola Tinubu ya fadi haka ne yayin ganawa da shugabannin majalisar tarayya da suka kai masa gaisuwar sallah.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bukatar canza tinani a Najeriya

Shugaban kasa Bola Tinubu ya ce duk da talaucin da ake fama da shi bai kamata 'yan kasa su juyawa Najeriya baya ba.

Bola Tinubu ya ce kamata ya yi mutane su zurfafa tunani kan yadda za su yi amfani da yanayin da ake ciki domin kawo cigaba a kasa.

Kada mu lalata kasar mu

Shugaban ya kara da cewa dabi'ar wasu yan kasa da suke fakewa da talauci suna lalata turakan wuta da sace karafun jirgin kasa ba abu bane mai kyau, rahoton jaridar Leadership.

Ya tabbatar da cewa yin hakan zai haifar da matsala ga tattalin arzikin kasa da kuma kara talauci kan wanda ake fama da shi.

Kara karanta wannan

Kwastam ta gano dabarar da dillalai suka kirkiro wajen shigo da haramtattun kwayoyi

Za a cigaba da yakar yan bindiga

Cikin bayanan da shugaban kasar ya yi ya ce gwamnati za ta cigaba da yakar 'yan bindiga da suke hana mutane noma a kasar.

Ya ce akwai barazana babba ga Najeriya matukar manoma ba su samu damar yin ayyukan gona yadda ya kamata ba saboda haka ba za suyi sakaci da lamarin ba.

Shehun Borno ya yi magana kan tsaro

A wani rahoton, kun ji cewa Shehun Borno ya magantu kan wasu garuruwa a jihar Borno da har yanzu suke ƙarƙashin ikon 'yan ta'addan Boko Haram.

Basaraken ya mika korafi ga shugaba Bola Tinubu da jami'an tsaro kan buƙatar kwato wuraren domin samun zaman lafiya mai dorewaa a jihar Borno.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Online view pixel