Sarautar Kano: Kwankwaso Ya Tona Asirin Masu Zuga Aminu Ado, Ya Fadi Shirinsu

Sarautar Kano: Kwankwaso Ya Tona Asirin Masu Zuga Aminu Ado, Ya Fadi Shirinsu

  • Yayin da ake ci gaba da rigimar sarautar Kano, Rabiu Kwankwaso ya zargi Gwamnatin Tarayya da neman kawo rudani
  • Kwankwaso ya ce wasu makiya suna ba gwamnatin shawara tare da nuna goyon baya ga Aminu Ado Bayero
  • Jigon jam'iyyar NNPP ya ce akwai wasu 'yan Boko Haram na zamani a Kano da ke neman rikita jihar gaba daya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Sanata Rabiu Kwakwaso ya zargi Gwamnatin Bola Tinubu da APC da neman dagula jihar Kano.

Rabiu Kwankwaso ya zargi gwamnatin ne game da halin da ake ciki yanzu inda ya ce suna jin shawarar makiyan Kano.

Kwankwaso ya zargi Gwamnatin Tarayya da rikita Kano
Sanata Rabiu Kwankwaso ya kalubalanci makiya jihar Kano. Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso.
Asali: Facebook

Kano: Kwankwaso ya zargi Gwamnatin Tarayya

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya shiga babbar matsala, jam'iyyar APC ta nemi jami'an tsaro su kama shi

'Dan siyasar ya bayyana haka ne yayin martani kan rigimar masarautun Kano a faifan bidiyo da hidimin Abba Kabir, Abdullahi Ibrahim ya wallafa a shafin X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce jami'an tsaron Gwamnatin Tarayya suna nuna goyon baya ga tubabben sarkin Kano, Aminu Ado Bayero.

Jawabin Rabiu Musa Kwankwaso

"Muna godewa gwamna kan kokarinsa wurin tafiyar da abubuwa musamman harkar Boko Haram na zamani da ke neman kawo rigingimu a jihar Kano."
"Ba za mu nade hannayenmu muna gani wasu makiyan Kano su kawo rudani tare da lalata zaman lafiyar jihar ba."
"Zamu tabbatar ba gwamna goyon baya domin ya samu nasara, mun gode Allah yana ayyukan alheri duk da tsaiko da yake samu."
"Wasu makiyan Kano da suka samu matsalar kwakwalwa ke ba Gwamnatin Tarayya shawara yadda za su kwace Kano wurin amfani da dokar ta baci."

Kara karanta wannan

Gwamna Abba ya aika da sako ga Tinubu ana cikin rikicin sarautar Kano

"Yayin da ake tunkarar 2027, wasu 'yan siyasa na neman lalata Kano, zamu yi mutuwar kasko da su kan mu bari su karasa mu babu dalili."

- Rabiu Kwankwaso

Kwankwaso ya caccaki 'makiya' Kano

Kwankwaso ya kalubalanci duka masu neman rikita jihar a siyasa da cewa NNPP ta shirya duk wani yaki da za a yi.

Ya ce ba su tsoron rasa mulki kuma za su ci gaba da zama 'yan siyasa ko da ba su kan mulki inda ya ce za su amince da tattaunawa amma ban da cin zarafi da bazarana.

Kwankwaso ya yabawa Abba Kabir

Kun ji cewa Sanata Rabiu Kwankwaso ya yabawa Abba Kabir kan irin kokarin da yake yi wurin inganta jihar Kano.

Kwankwaso ya ce duk da neman rikita Kano da ake yi amma gwamnan ya yi abin da zai yi na kawo ci gabaa jihar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.