Sarki Muhammadu Sanusi II ya Fadi Abin da Yake Nema Daga Jama'a Bayan Rasuwarsa

Sarki Muhammadu Sanusi II ya Fadi Abin da Yake Nema Daga Jama'a Bayan Rasuwarsa

  • Sarkin Kano na 16 Muhammadu Sanusi II ya na fatan jama'a za su tuna shi a matsayin shugaba na gari kuma su yi masa addu'a bayan ya koma ga mahaliccinsa a nan gaba
  • Ya bayyana fata haka ne a lokacin da dambarwar masarautar Kano ta dabaibaye shi da dan uwansa, kuma sarki na 15, Aminu Ado Bayero baya dawo da shi karagarsa
  • Sarki Sanusi II ya ce abu daya cikin biyu ne ke samun shugabanni, ko dai a zage su da munin aikinsu, ko a yabe su da alherinsu kuma shi addu'a ya ke fatan ta raba shi da jama'a

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Kara karanta wannan

Yaron Sanusi II yayi magana da kotu ta saurari shari’ar Aminu Ado Bayero

Kano- Sarkin Kano na 16, Malam Muhammadu Sanusi II ya bayyana yadda ya ke son al'umma su tuna shi bayan ya koma ga mahallici.

Gwamnatin Kano karkashin Abba Kabir Yusuf ce ta dawo da shi karagarsa bayan tsohon gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya sauke shi.

Sanusi II
Sarki Sanusi II ya bayyana fatan samun addu'o'i da fadin alkhairi a kansa bayan ya rasu Hoto: Sanusi Lamido Sanusi
Asali: Facebook

A wata hira da ya kebanta da Vanguard News, Sarki na 16 wanda rikicin masarauta ya dabaibaye shi ya ce ya na fatan mutane ba za su zage shi bayan rasuwarsa ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Ina son shaida mai kyau," Sanusi II

Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya ce daya daga burin da ke zuciyarsa shi ne samun shaida mai kyau idan ya rasu.

Ya ce;

"Ina son idan mutane sun tuna da ni su ce mutumin kirki ne."

"Shugaba yana shan yabo ko suka" - Sanusi II

Kara karanta wannan

Masarautun Kano: Sanusi II ya fadi musabbabin tuge shi da Ganduje ya yi daga sarauta

Sarkin ya kara da cewa matukar mutum zai shugabanci al'umma, dayan biyu ne – ko dai a zage shi ko kuwa a yabe shi.

Sanusi II ya ce amma fatan da yake yi shi ne bayan ya bar duniya, mutane su fadi alkhairinsa, tare da yi masa addu'a.

Yanzu dai hankulan jama'a sun rabu a sakamakon maido Khalifan na Tijjaniya.

"Siyasa ta sa Ganduje cire ni," Sanusi II

A wani labarin mun kawo mu ku cewa Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II ya fadi dalilin da tsohuwar gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta tsige rawaninsa sa baya.

Ya ce tsohon gwamna Ganduje na zarginsa a wancan lokaci da kin yi masa biyayya, wanda Sanusi II ke ganin ba kwakkwaran dalili ba ne na tsige sarki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.