Gwamnatin Tinubu ta yi Biris da NLC, ta Dage a kan Biyan Ma'aikata N62,000

Gwamnatin Tinubu ta yi Biris da NLC, ta Dage a kan Biyan Ma'aikata N62,000

  • Gwamnatin tarayya ta dage kan cewa ba za ta iya biyan ma'aikatan kasar nan abin da ya haura N62,000 a matsayin mafi karancin albashi ba duk da kiraye-kirayen kungiyar kwadago
  • Shugaban kwamitin gwamnati da ke duba kan mafi karancin albashi, Bukar Goni Aji na ganin kungiyoyin kwadago sun so kansu idan suka matsa a kan a biya abin da ya haura haka
  • Kungiyar kwadag ta NLC da 'yan kasuwa TUC na bukatar gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta amince da biyan N250,000 a matsayin mafi karancin albashi, kuma shi ne tayinsu na karshe

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Abuja- An ja daga tsakanin kungiyar kwadago ta kas (NLC) da gwamnatin tarayya kan batun mafi karancin albashi yayin da gwamnatin ta dage kan cewa ba za ta taba iya biyan abin da yah aura N62,000 ga ma’aikatan kasar nan ba.

Kara karanta wannan

NLC, TUC sun aika sabon gargadi ga Tinubu kan mafi karancin albashi

Wannan na zuwa kwanaki kadan bayan kungiyar kananan hukumomi ta shaidawa gwamnatin tarayya cewa ba za su iya biyan ma’aikatansu N62,000 saboda ba su da kudin yin hakan.

NLC da gwamnati
Gwamnatin tarayya, NLC sun gaza cimma matsaya kan N62,000 mafi karancin albashi Hoto: @NLCHeadquarters
Asali: Twitter

Kungiyar NLC ta raina albashin N62, 000

Punch News ta wallafa cewa a ranar Talata, 28 Mayu, 2024 ne aka sake samun rashin fahimta tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyar kwadago da ma’aikatu masu zaman kansu kan biyan ma’aikata akalla N62,000.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

NLC na ganin rainin hankali ne sosai gwamnati ta yi masu tayin N62, 000 idan aka kwatanta da yanayin da farashi yake kara hauhawa a kasuwannin Najeriya da ma sauran bukatu irinsu kudin wuta da ruwa.

“Gwamnati ba ta san wahala ba,” NLC

Kungiyar kwadagon kasar nan ta yi martani ga kwamitin gwamnatin tarayya karkashin jagorancin Bukar Goni Aji da cewa an gwamnati ba ta san ‘yan kasar nan na shan wahala ba, kamar yadda Vanguard News ta wallafa.

Kara karanta wannan

'Me ma'aikata za su yi da albashin N62,000?' NLC ta yi watsi da sabon tayin gwamnati

Kungiyoyin kwadago dai na neman gwamnatin tarayya ta amince da biyan mafi karancin albashin N250,000 wanda daga shi ne su ka ce ba za su kara sassautawa ba.

An samu masu goyon bayan kungiyar kwadagon kamar Anglican Communion da ke ganin akwai bukatar biyan ma’aikata abin da zai wadacesu biyan bukatun rayuwa, lamarin da har yanzu kusoshin gwamnati ke ganin ba za su iya ba.

Gwamnan Anambra ya bada shawara kan albashi

A wani labarin kun ji cewa gwamnan jihar Abia, Charles Suludo ya bayar da shawara kan abin da ya kamata a rika biyan 'yan siyasa a Najeriya yayin da ake tsaka da tattauna albashin ma'aikata.

Farfesa Soludo na ganin abin da ya fi kamata shi ne gwamnatin tarayya ta fara biyan 'yan siyasa mafi karancin albashin da za ake ta kokarin sai ta biya ma'aikatan Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Online view pixel