Bikin Sallah Ya Koma Makoki Bayan Mutuwar Wasu Mutane a Hadarin Mota

Bikin Sallah Ya Koma Makoki Bayan Mutuwar Wasu Mutane a Hadarin Mota

  • Ana cikin bikin babbar sallah wani mummunan hadarin mota ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da jikkata wasu a jihar Ogun
  • Kakakin hukumar kiyaye hadura ta kasa (FRSC) a jihar Ogun, Florence Okpe ta tabbatarwa manema labarai faruwar hadarin
  • Florence Okpe ta bayyana dalilin da ya jawo hadarin da irin asarar rayuka da aka tafka biyo bayan faruwar lamarin a jiya Lahadi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Ogun - An samu mummunan hadarin mota yayin da al'ummar Musulmi ke tsaka da hidimar babbar sallah.

Rahotanni sun nuna cewa hadarin ya yi sanadiyyar mutuwar mutane tare da jikkata wasu da dama.

Hadarin mota
Hadarin mota ya kashe mutane a jihar Ogun a ranar sallah. Hoto: Federal Road Safety Corps Nigeria.
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa hadarin ya faru ne a yankin Osasa kan hanyar Sagamu-Ijebu Ode a jihar Ogun.

Kara karanta wannan

Ana bikin sallah, 'yan bindiga sun tafka kazamar ta'asa a Sokoto, sun sheke mutum 10

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mutanen da suka mutu a hadarin

Kakakin hukumar kiyaye hadura ta kasa (FRSC) a jihar Ogun, Florence Okpe ta tabbatar da cewa mutane biyu sun mutu a sanadiyyar haɗarin.

Florence Okpe ta tabbatar da cewa daga cikin mutanen da suka mutu akwai mace daya da namiji daya.

Waɗanda hadarin ya jikkata

A cikin bayanan da hukumar FRSC ta fitar ta nuna cewa mutane uku sun jikkata a sanadiyyar hadarin, rahoton PM News.

Hukumar ta kuma tabbatar cewa an mika wadanda suka jikkatan zuwa asibitin Ijebu Ode domin jinya da karbar magani.

Menene abin da ya jawo hadarin?

Florence Okpe ta tabbatarwa manema labarai cewa hatsarin ya faru ne da misalin 11:28 na safe a jiya Lahadi a lokacin da ake dawowa daga sallar idi.

Ta kuma kara da cewa hatsarin ya faru ne sakamakon gudun da ya wuce ƙima da matuƙan motocin da suka yi karo da juna suke yi.

Kara karanta wannan

Hajji 2024: Hukumomin Saudiyya sun kwamushe mutum 18 bisa karya dokar aikin Hajji

Sanusi II ya tura sakon sallah ga Kanawa

A wani rahoton, kun ji cewa sarkin Kano na 16 ya ba Musulmi shawarin su taimaki juna a yayin bikin babbar sallah da ake ci gaba da yi a duniya.

Muhammadu Sanusi II ya kuma yi kira ga jama’a da su rungumi zaman lafiya da kaunar juna tare da komawa ga Allah don neman zaman lafiya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Online view pixel