InnalilLahi: Ana Shirin Babbar Sallah Wasu Mutum 19 Sun Mutu Lokaci Guda a Arewa

InnalilLahi: Ana Shirin Babbar Sallah Wasu Mutum 19 Sun Mutu Lokaci Guda a Arewa

  • Wani mummunan hatsarin mota ya yi ajalin mutane 19 yayin da wasu biyar suka samu raunuka a kauyen Kanbi da ke jihar Kwara
  • Mai magana da yawun hukumar kiyaye haɗurra FRSC, Olusegun Ogungbemide ya ce gudun wuce ƙima da tsere suka haddasa haɗarin
  • Kwamandan FRSC na jihar Kwara ya umarci jami'ai su kara matsa ƙaimi wajen sintiri domin daƙile yawan take dokokin tuƙi a tituna

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kwara - Mutane 19 sun mutu yayin da wasu biyar suka samu raunuka a wani hatsarin mota da ya afku a kauyen Kanbi, sabon titin Jebba a jihar Kwara.

Hatsarin, wanda ya auku da misalin karfe 8:00 na daren jiya Alhamis, ya rutsa da wata motar Tirela da farar bas Toyota Hiace mai lamba LSD363YE.

Kara karanta wannan

Gwamna ya cire girman kai, ya koma aji domin ƙarasa karatun digiri a jami'ar Najeriya

Taswirar jihar Kwara..
Hadarin mota ya yi ajalin mutane 19 a jihar Kwara
Asali: Original

Mai magana da yawun hukumar kiyaye haɗurra (FRSC), Olusegun Ogungbemide, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa ranar Jumu'a, 14 ga watan Yuni.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ogungbemi ya ce binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa hadarin ya faru ne sakamakon gudun wuce ƙima da tsere, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Mutum 19 sun rasa rayuwarsu a Kwara

Ya ƙara da cewa haɗarin ya rutsa da mutane 25 wanda suka ƙunshi maza 13, mata biyar da kuma ƙananan yara bakwai.

Ya ce:

"Mutum biyar daga ciki sun samu raununa, maza uku da mata biyu yayin da mutane 19 suka rasa rayuwarsu a haɗarin. A halin yanzun an kai waɗanda suka ji rauni asibitin Orisun Ayo."
"An ajiye ɗaya daga cikin gwarwakin a wannan asibiti, sauran mutum 18 kuma ƴan uwansu sun zo sun ɗauke su domin yi masu janaza."

Kara karanta wannan

Bola Tinubu ya ɗauki matsaya, zai miƙa sabon mafi ƙarancin albashi ga majalisa

Ogungbemide ya ce shugaban hukumar FRSC, Shehu Mohammed, ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda direbobi ke tuƙin ganganci a kan manyan tituna, cewar rahoton Leadership.

FRSC ta fara ɗaukar mataki

A cewarsa, ƙaruwar tukin ganganci tare da take dokokin hanya abin damuwa ne duba da yadda hakan ke jefa rayuwar bayin Allah cikin haɗari har wasu su mutu.

Sakamakon haka babban kwamandan FRSC ya umarci manyan jami'an kiyaye haɗurra su ƙara zage dantse wajen ayyukan sintiri domin magance yawan haɗurra.

Ƴan daba sun tada hayaniya a Kano

A wani rahoton kuma Ƴan daba sun tayar da hargitsi a kasuwar da ke Masallacin idi a Kano bayan gwamnatin jihar ta umarci mutane su tashi.

Gwamnatin Kano ta bai wa ƴan kasuwar wa'adin sa'o'i 48 su tashi daga wurin, amma har yanzu ana ci gaba da hada-hada.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262